Indiyawa Sun Fara Murnan Zuwan Zakzaky Kasar Su
INDIYAWA SUNA MURNA DA ZUWAN MALAM ZAKZAKY QASAR SU
Tun bayan da babbar kotun jihar Kaduna ta bai wa jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa, damar tafiya kasar Indiya domin neman magani, wasu Indiyawa suka "fara" murna da zuman nasa.
Sun kirkiri wani maudu'i a shafin Twitter na #IndiaWelcomesZakzaky da ke nufin India na maraba da Zakzaky.
A safiyar jiya Litinin ne dai kotun ta bai wa mutanen biyu damar zuwa kasar ta Indiya domin neman magani, kamar yadda lauyoyinsa suka nema.
Damar da babbar kotun ta Kaduna ta bai wa Sheikh Ibrahim Zakzaky ta fita kasar waje tana tattare da wasu sharudda da kotun ta ce lallai sai an cika su.
Daya daga cikin sharuddan shi ne dole ne jami'an gwamnati ne za su yi wa Zakzaky da matarsa rakiya zuwa Indiya.
Tun bayan kama shi a Disambar 2015, Indiyawa mabiya Shi'a sun bi sahun takwarorinsu na wasu kasashe musamman a yankin Gabas ta Tsakiya da Tekun Fasha, wurin nuna goyon baya a gare shi a shafukan saza zumunta.
Wannan ne ya sa wasu 'yan Indiya suke ta faman murna cewa mutumin da suka dade suna fafutukar neman a saki, yanzu zai je kasarsu domin neman magani.
No comments