Hajji Kiran Allah ~ Karanta Kaji Abun Mamaki, Labarin Wani Tsoho Da Allah Ya Kirashi Kasa Mai Tsarki - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Hajji Kiran Allah ~ Karanta Kaji Abun Mamaki, Labarin Wani Tsoho Da Allah Ya Kirashi Kasa Mai Tsarki



    Hajji Kiran Allah

    A nan wani mutumi ne talaka tubis  dan kasar Ghana, wata rana dan karamin jirgin daukar hoto na kamfanin Dillancin Labarai na Kasar Turkish ya fado a  kan bunun gidansa, a lokacin da yan jaridar kasar Turkish din suke kokari hada wani rahoto a kasar.

    Allah cikin ikonSa jirgin ya fado gidansa ya tsinta, sai yan jaridar suka zo nema, ya kau fito masu da shi a hannu, ya mika masu cikin raha yake ce masu, baku da babban jirgin da zai dauke ni zuwa Makka na yi aikin Haji?

    Yan jaridar nan suka yi dariya suka amshi dan jirginsu, sai kuma suka watsa abin da ya afku tsakaninsu da shi a kafafen sadarwar, Wanda a yanzun haka an bayyana cewa gwamnatin kasar ta biya masa aikin Hajin ya cika burin abin da yake mafarkin yi tsawon rayuwarsa, duk da Allah bai ba shi hali na dukiya ba, amma Allah Ya sawake masa hanya cikin  sauki

    Abin da labarin ya koyar
    Idan Allah Ya nufe  ka da samun alkairi, a duk irin cikin halin da kake, sai Allah Ya hore maka da hanya mafi sauki ta samun wannan alherin wadda wayauka da tunanin ka ba za su taba bijiro maka da hakan ba.

    No comments