Bayan Shekara Hudu Da Daura Aure Amarya Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi Ta Tare A Ranar Asabar
Shekaru hudu da daurin auren, sai a yanzun ne Amaryar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta hudu ta sami tarewa a gidansa.
A ranar Asabar ce aka kawo Sarauniya Sa’adatu Barkindo Mustapha, fadar ta Sarkin Kano, inda aka gudanar da al’adar nan ta budar kai a ranar Lahadi.
Sabuwar Amaryar dai ta Sarkin na Kano, a kwanan nan ne ta kamala karatunta daga wata Jami’a da ke kasar Ingila, inda ta ta fi jim kadan da daura auren nasu.
Idan dai ba a manta ba, Sarki Sanusi II na Kano, ya auri diyar Mai Martaba Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo-Mustafa, ce a wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a Yola, a watan ranar 25 ga watan Satumba, 2015.
Amaryar Sanusi din ta hudu, ta na da shekara 18 ne a lokacin da ta ke karatunta na sakandare a ka daura auren.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ne ya wakilici Sarkin na Kano, a wajen bikin, sa’ilin da Gwamnan Jihar ta Adamawa na wancan lokacin Jibrilla Bindow, ya kasance a mazaunin uban Amarya, wanda ya bayar da aurenta.
A wancan lokacin Sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II, yana kasar Saudiyya a matsayin jagoran Mahajjatan Nijeriya, zuwa aikin Hajji na waccan shekarar.
Sarki na Kano, Muhammadu Sanusi II, yana da wasu matayen auren guda Uku, sune kuwa matarsa ta farko wacce diya ce ga Marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, Sadiya, Maryam da Rakiya.
No comments