Rahama Sadau Ta Murnan Zagayowar Ranar Haihuwanta
Rahama Sadau wata Jaruma ce a kasar Najeriya wadda tayi fice wajen a fannin wasan kwaikwayo na masana’antar Kannywood. An haifi Sadau a ranar 7 da watan Disamba na shekara ta alif dari tara da casa’in da uku (7 December 1993) a unguwar Sarki dake cikin garin Kaduna na Jihar ta Kaduna a Najeriya.
Kasancewa JarumaJaruma Rahama Sadau wacce take rike da kambu na karatun Kasuwanci daga Foliteknic ta Kaduna ta samu shiga masana’antar Kannywood a shekarar 2013. Sadau ta kasance daya tilo wajen tafka mahawara a cikin yaren Hausa, Turanci da Indiyanci baki daya. Jaruma Sadau ta samu fice bayan fitowar ta a wani shiri mai suna “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu.
Lambar Yabo da ta Girma
Jaruma Sadau ta samu lambonin girma da yabo daban daban a kasar Najeriya dama kasashen ketare da dama wanda ya hada da Jaruma ta musamman a shekara ta 2014 da kuma 2015 wadda ta samu daga City People Entertainment Awards. Bugu da kari ta samu award din African Film Awards a shekara ta 2015 wanda African Voice ta hada.

Aikin GidauniyyaGidauniyar Rahama Sadau mai suna Ray of Hope a turance tayi fice wajen shiga shirye shirye na masu ciwon daji mai suna Cancer da turanci wanda Medicaid sukan shirya a lokaci lokaci. Sannan a wani lokaci a baya ta samu ziyartar gidan ‘yan gudun hijira dake garin Wasa a babban birnin Abuja a Najeriya.
Ku Kasance Tare Da Shafin Mu Domin Samun Labarai Da Dumi-duminsu.
Ku Kasance Tare Da Shafin Mu Domin Samun Labarai Da Dumi-duminsu.
No comments