Wai Shin Da Gaske Ne Auren Jaruma Sadiya Kabala Ya Mutu? - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Wai Shin Da Gaske Ne Auren Jaruma Sadiya Kabala Ya Mutu?


    Auren Jaruma Sadiya Kabala ya mutu, daya daga cikin futattun jaruwa mata da akeji dasu a masana,antar fina-finan hausa wayanda sukayi aure a wannan shekaran.

    Jarumar tayi aure ne watanni uku da suka gabata wanda yanzu haka auren nata ya mutu tana zaman zawarci.

    Kwanakin baya mutane nata tambaya game da auren nata, wai shin ya mutune ko dai yana nan saboda yanayin yadda sukaga ta koma harkokokinta kamar ba matar aure ba.


    Jarumar kwanakin baya ta wallafa wani hoto nata da wani saurayi a shafinta na Instagram harma kuma take wasu kalamai wayanda suka shafi soyayya wannan ne ya ya jawo hankalin mutane har suka fara cece-ku-ce.

    saboda bai kamata ace matar aure tana irin wayan abubuwa da wani wanda ba muharraminta ba.


    Shafin Noth Blog na Instagram ya wallafa wannan hoto nata dan tabbatar da gaskiyar al'amarin zargin da mutane sukyi kan cewa auren nata ya mutu.

    Amma kuma kuma daga bisani jarumar ta fita ta karyata cewa aurenta bai mutu ba harma da wasu daga cikin kawayenta sun tabbatar da cewa auren nata bai mutu ba.

    Kwatsam kuma sai gashi wata jarida ta wallafa tabbacin mutuwar auren nata bayan wata uku dayinshi.

    Ku kasance da shafin hausa22blog.com domin samun labarai da dumi-duminsu.

    No comments