Ko Na Mutu Ku Gayawa Mahifiyata Kadda Tayi Kuka
Shi Yarubuta Da Kansa!
"Kufadawa Mahaifiyata Kartai Kuka"
Dan Allah 'yan uwa ina bukatar addu'arku, sati 3 ina cikin tsanani babu network yanzunema nasamu damar yin wannan postin din da network yazo, yanzu haka ina garin gambaru ngala a jahar borno, sakamakon harin da 'yan boko haram suka kaimana. Saboda haka yanzu bani da hanyar tsira.
Sun bubbunne boma-bomai ahanyar danake tinanin zan'iya tsira. Koda ace bansamu damar tsiraba, kufadawa babata kartai kuka, nayi iya bakin kokarina. Allah shiyasan dalilin faruwar hakan... Ni sojane. Inai muku godiya gaba daya dakuka sani a addu'a dakuma share din sakona.
Source By: Kano State Media



No comments