Kannywood Idan Rara Zai Shekara 100 Akan Mukamin Da Buhari Ya Bashi Bazai Samu Abunda Nake Dashi Ba - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Kannywood Idan Rara Zai Shekara 100 Akan Mukamin Da Buhari Ya Bashi Bazai Samu Abunda Nake Dashi Ba


    Shahararren Mawakin Hausa da ake yi wa lakabi da Sarkin Waka Nazir M Ahmad wanda sauran Mawakan Hausa ke yayin kwaikwayon salon wakarsa.

    Ya bayyana cewa, idan da Mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara zai yi 100 a mukamin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba shi.

    Na Daraktan Kida da Waka na kasa ba zai mallaki abinda Naziru ya mallaka ba.

    Nazirun yayi wannan furuci ne ga masu cewa yana hassada ne saboda mukamin da aka baiwa Rarara.

    Saboda ya ce sun yi wa Buhari da APC halacci ba a biya su ba. Naziru ya basu amsar cewa shi be ma san da wannan magana na ba wa Rarara mukami ba sai a bakinsu.
    Kuma shi Allah Ya tsare shi da yin hassada akan abinda zai kare a Duniya, yace, ga manyan mutane da zai yi hassada a kansu sai shi (Rarara)? Ya kara da cewa ko shekara dari zaiyi akan mukamin da aka bashi ba zai samu irin abinda gare shi ba.

    Daga: Fb/Sarauniya

    1 comment: