Wata Sabuwar Kungiya Tayi Alkawarin Bawa Buhari Kuri'u 40 Milliyan A Zaben 2019
Wata kungiyar masoya shugaban kasa da mataimakinsa Osinbanjo mai suna ‘Buhari Osinbajo Dynamic Support Group’ ta sha alwashin samar wa shugaban kasa Buhari da Osinbanjo masu kada kuri’a sama da mutum miliyan arba’in a zaben da ke tafe na 2019..
Ko’odinetan kungiyar a shiryar Arewa Maso Gabas, Alhaji Musa Ahmad Azare shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke zantawa da ‘yan jaridu a shekaran jiya jimkadan bayan kammala tsara wani gangamin wanda jami’an ‘yan sanda suka hana gudanar shi domin wayar da kan jama’an shiyyar Arewa Maso Gabas dangane da sake zaben Buhari, taron wanda ya gudana a karamar hukumar Azare.
Ya ce, “Kawo yanzu mun samu tabbacin mutane sama da miliyan 20 da suka shaida mana za su zabi Buhari da Osinbanjo a zaben da ke tafe,” In ji shi. Ya ce, makasudin shirya gangamin wayar da kan jama’an dai shine domin su sake tunatar da magoya bayan shugaban kasa Buhari dangane da mallakar katin zabe na dindindin wacce da shine za su samu nasarar zaben Buharin da suke so din. Ya ke shaidawa, “Sannan kuma muna wayar wa jama’a da kan dangane da muhimmancin sake zaben Buhari a babban zaben da ke zuwa,” Ya shaida.
Ya kara da cewa, Buhari ya cancaci ‘yan shiyyar Arewa Maso Gabas su yi umumu su sake zaben Buhari duba da dumbin alkairan da ya samar musu kama daga ci gabantar da tattalin arziki, magance matsalolin tsaro hadi da soyayyar da ke yi wa yankin, “Ya kaddamar da shawo kan matsalolin tsaro a wannan yankin don haka muna son a sake bashi zarafi ya samu kaiwa ga kammala aikace-aikacen da ke kansa.
Sannan ku duba yadda ya samar da hukumar ci gaban arewa maso gabas wanda wannan hukumar kowa ya yi ittifakin zai kawo wa yankin nan gagarumar ci gaba,” In ji shi Musa Azare. Ko’odinetan ya bayyana cewar Buhari ya baiwa matasa zarafi da goyon baya gaya a mulkinsa inda ya shaida cewar Buharin ya aza tubalin gina kasa don haka da bukatar a mara masa baya ya kai ga ida daidaita kasar nan. Musa Azare ya kuma yi amfani da wajen dandamalin inda ya gode wa shugaban kasa Buhari dangane da sanya hanu kan kudurin baiwa matasa zarafin shiga a dama da su a harkokin siyasa, yana mai shaida cewar hakan na daga cikin soyayyar da ke da shi ga matasan kasar ne, “A bisa soyyar da ke yi wa matasa ne ma ya sanya kuka ga dandazon matasan sun hallara a wannan karamar hukumar domin nuna kaunarsu ga Buhari,” Ya ce.
No comments