Africa Ne Taci Kofin Duniya Ba Faransa Ba Nicole's Maduro - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Africa Ne Taci Kofin Duniya Ba Faransa Ba Nicole's Maduro



    'Yan Afirka Ne Ainahin WaÉ—anda Suka Ci Gasar Kofin Duniya - Shugaban Kasar Venezuela

    Cikin 'yan wasa 23, 16 'yan Afirka ne

    Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

    Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya bayyana cewar ya yi imanin Afirka ce, ba Faransa ba ta lashe gasar Kofin Duniya na 2018 da aka buga a kasar Rasha.

    Kasar Faransa ta lallasa Croatia da ci huÉ—u da biyu a wasan karshen da suka buga a birnin Moscow, amma da 'yan wasan da tsatsonsu na ainahi Afirka ne.

    "Tawagar Faransa na kama da tawagar Afirka. A zahiri Afirka ce ta yi nasara, 'yan ci ranin Afirka a kasar Faransa," Maduro ya bayyana a wani taro na bikin ranar 'yan sandan Venuzuela a ranar Litinin.

    "Wana irin tsana ce basu nuna wa Afirka ba, amma a gasar kwallon kafa ta Kofin Duniya Faransa ta lashe gasar, godiya ga 'yan wasan Afirka, ko kuma 'ya'yan 'yan Afirka."

    Biyu daga cikin waÉ—anda suka ci wa Faransa kwallo a wasansu da Croatia tsatson Afirka ne: Iyayen Paul Pogpa 'yan kasar Guinea ne, inda su kuma na Kylian Mbappe 'yan Kamaru da Algeria ne.

    Game da 'yan wasan da suka fara buga wasan karshe, Samuel Umtiti a Kamaru aka haife shi, iyayen Blaise Matuidi 'yan Angola da Congo ne, iyayen N'Golo Kante 'yan Mali ne, yayinda mahaifin Varane yake É—an Caribbean island na Martinique.

    Daga cikin tawagar mutum 23, guda 16 tsatson Afirka ne, duk da cewa kaftin Hugo Lloris, Antonio Griezmann da kuma É—an wasan gaba, Olivier Giroud, tsatson Turai ne.

    Duk da hakan dai Moduro ɗin ya taya tawagar faransa farin cikin nasarar da suka samu, sannan ya jinjina wa abokinsa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin karbar bakuncin gasar Kofin Duniya ɗin da ba a taɓa buga irin ta ba.

    No comments