An Rage Farashin Aure A Jihuriyar Niger Daga Jaka 50 Zuwa Jaka 20 - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    An Rage Farashin Aure A Jihuriyar Niger Daga Jaka 50 Zuwa Jaka 20




    Sarkin Damagaram, Mai Martaba Alhaji Abubakar Sanda, ya sanar da rage farashin sadakin mata A masarautar sa ta Damagaram a jamhuriyyar Nijar
    Sarkin ya sanar da hakan a lokacin da ya halarci wani taro na masu ruwa da tsaki,

    wanda ya hada da 'yan kasuwa da kuma kungiyoyin mata a jihar ta Damagaram,

    Sarkin ya ce masarautar ta dauki wannan kudurin ne bayan jama'ar garin sun kai masa kukansu akan a sama musu sauki akan al'amuran da suka shafi aure da bikin suna da kuma wasu manyan bidi'oi a yankin jihar. Wanda a cewar sa hakan ya sanya maza basu iya aure sosai kuma mata suna ta karuwa babu mazaje, Sarkin yace wannan ragin zai rage yawan yan mata marasa aure

    A yanzu haka dai, masarautar ta garin Damagaram ta rage kudin sadakin aure daga jaka 50 zuwa jaka 20, sannan kuma masarautar ta hana daukan amarya a cikin jerin gwanon motoci, sannan an rage kayan gara, daga karshe kuma an hana yin ankon biki kwata-kwata a jihar. Duk dai da nufin samar da sauki cikin sha'anin aure,

    No comments