Amarya Ta Sokawa Mijinta Wuka Bayan Sati Biyu Dayin Aurensu A Kaduna - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Amarya Ta Sokawa Mijinta Wuka Bayan Sati Biyu Dayin Aurensu A Kaduna



    Wata Amarya ta sokawa mijinta wuka a ciki sati biyu da yin Aure a Kaduna
    Daga Hausa Times. 
    Wata mata ta sokawa mijinta wuka Sati Biyu da yin aure a kauyen Kyadi dake karamar hukumar Kudan a jihar Kaduna.
    Hausa Times ta ruwaito lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Laraba da ta gabata.
    Wani jami’in hukuma wanda ya tsaya a lokacinda aka kai mijin matar a babban asibitin garin yace magidancin ya rayu a yayinda ita kuma matar aka kama ta kuma yanzu haka tana hannun hukuma.
    Hausa Times tayi kokarin fadada bincike akan faruwar lamarin sai dai jami’in yace ‘ba hurumina bane in baku duka amsoshin da kuke bukata amma dai binciken farko ya nuna cewa auren soyayya sukayi’
    Ya cigaba da shaidawa Hausa Times cewa ‘sati biyu da yin aure sai amaryar ta rika guduwa gidansu har dai takai ga mijin nata da danginta sun yi mata fada.
    Yace ‘shine a wannan karon bayan an dawo da ita sai ta fara hada kayanta wai zata gudu tabi duniya domin ita ba zata zauna da angon nata ba.’
    ‘Bayan sunyi cacar baki da mijin nata mai suna Danladi ta fadi mashi zata tsere ta shiga duniya sai ya yi mata fada har ta nuna komi ya wuce ya koma daki ya kwanta ashe ta fakeshi ne, bayan ya koma daki ya kwanta kawai sai ta shiga da wuka ta soka masa sannan ta fita daga gidan a guje da wukar a hannunta’
    Hoton da kuke gani dai na mijin ne wato Danladi ana yi mashi aiki bayan an kaishi wani asibitin kudi dake Makarfi.
    Hausa Times ta ruwaito bayan ta soka masa wukar sai ta fito a gigice tana gudu da wukar a hannu a yayinda shi kuma mijin yayi ta ihu lamarin da yasa aka farga da abunda ke faruwa har matasa suka iya kama ta suka mikawa yan sanda a yayinda shi kuma aka daukeshi zuwa wani asibitin kudi dake Makarfi.

    No comments