Yadda Maryam Ta Samu Nasarar Kaiwa Mijinta Hari Yayin Da Yayi Kabbarar Sallar Isha,i
Yadda Maryam ta kashe mijinta yana sallah
A yayin da ake cigaba da juyayin rikicin ma’auratan nan da ya jawo matar ta kashe mijinta, wasu rahotanni sun bayyana cewa ashe matar mamacin ta samu nasarar soka masa wuka ne sa’ilin da ya kabbara Sallar isha’i
Majiyar Hausa Times ta ruwaito wani Makusancin dangin marigayi Bilyaminu Bello, ya shaida masu cewa a ranar Asabar da daddare, rikici ya barke tsakanin Maryam da maigidan nata bayan ta karanta wasu sakonnin tes a wayar mijinta, wadan da suke dauke da kalaman soyayya, abinda yake tabbatar mata da cewar, yana soyayya da wata daban a waje.
Jaridar Daily Nigerian a hirar da tayi da wani makusancin mamacin, yace, sun yi zaton sabanin da aka samu tsakanin ma’auratan biyu ya wuce, lokacin da Kawun Maryam din ya shiga cikin al’amarin domin sasantawa.
Kamar yadda ya shaidawa majiyar tamu, Maryam ta samo sharbebiyar wuka a dakin girki (kitchen), sannan ta jira lokacin da mijin nata ya kabbara Sallar Isha, sannan ta kaddamar masa da mummunan hari, inda ta sassoka masa.
“A lokacin da ta soke shi a bayansa da kirjinsa da kuma ‘ya ‘yan marenansa, nan take ya fadi kasa yana marari tare dafatan ta taimake shi. Maryam na kallonsa, kwance male-male cikin jini, yana rokonta da ta taimaka masa don ceton rayuwarsa.
“An jiyo shi yana cewar ‘Maryam ki taimake ni… Maryam ki taimake ni, har ya kai gargarar mutuwa yana kiran da ta agaje shi, amma shiru tayi tsaye tana kallonsa, har ya kasa yin wani katabus, sannan ta bara.
“Maryam kawai cewa take, Allah ne ya tona maka asiri, tana maimaitawa, har ya rasu a wajen.
“Awa daya bayan wannan dambarwa ta auku, lokacin da taga baya ko motsi, sannan ta nemi taimakon makota da su taimaka mata a sanya shi a cikin mota domin ta kaishi asibiti.
“Asibitin farko da suka je, sun ki yadda su duba shi sabida halin da suka ganshi suka ce sai da dan sanda, sai da suka je wani asibitin ne,sannan jami’an asibitin suka kirawo ‘yan sanda, kuma Maryam ta tabbatar da cewar ita ce ta cakawa mijin nata wuka har ya mutu” A cewar dangin mamacin.

No comments