Hukumar Gudanar Da N-Power Ta Fitar Da Sunayen Wayanda Suka Samu Nasara
Hukumar Gudanarwar N-Power Ta Fitar Da Sunayen Wadanda Suka Samu Nasarar Fitowar Sunayensu Na Wannan Shekarar (2017 Npower Applicants) A Shafinta Na Yanar Gizo.
An fitar da sunayen ne jiya Litinin da misalin karfe 11:30pm na dare, duk wanda ya san ya cika neman gurbin kuma ya rubuta jarabawar da aka gudanar a yanar gizo, to zai iya duba sunansa ko Allah ya sa ya dace.
Ga hanyoyin da mutum zaibi domin duba sunansa
1. Ka rubuta wannan adireshin a komfutar ka ko wayarka idan ka shiga opera ko Google Chrome ko Mozilla www.npower.gov.ng saika danna enter ko go
2. Bayan ka danna shafin zai bude zakaga inda aka rubuta "check your pre-selection status " wato ana nufin ka latsa wannan wurin domin sunanka
3.bayan ya bude kuma zakaga inda akace ka rubuta lambar wayarka ko lambar BVN taka. Saika latsa wurin ka saka lambar taka sannan saika latsa inda aka rubutu Good luck ta koren rubutu
4. Bayan ka danna koren rubutun ne na'ura zata fara binciken sunanka, idan kayi nasara na'urar zata nuna sunanka tareda tayaka murna
5. Daga baya kuma zaka iya samun sako daga hukumar ta Npower mai nuni da kayi nasara kuma suna tayaka murna
6. Abu na gaba kuma shine, saika shirya dukkanin takardun ka ka aje domin zuwa fara tantancewa wanda za'a fara insha Allahu ranar 27/11/2017 har zuwa 8/12/2017
Allah yaba mai rabo sa'a
Idan kuma kana samun wata matsala wajen duba sunayen, zaka iya kiran daya daga cikin wadannan lambobin wayar
MTN
09060000445
09060000446
09060000447
09060000448
09060000449
09060000450
09060000451
09060000452
09060000453
09060000454
GLO
09055555960
09055555961
09055555962
09055555963
09055555964
09055555965
ETISALAT
09099998401
09099998402
09099998403
Source By Rariya

No comments