Kannywood Ban Auri Hadiza Gabon Ba (Ali Nuhu)
Ban Auri Hadiza Gabon Ba, Inji Ali Nuhu
Shahararren Jarumin finafinan Hausa, Ali Nuhu ya musanta zargin dake yawo cewar wai ya auri abokiyar aikinsa Hadiza Gabon.
Dan wasan ya karyata zargin ne yayin da yake zantawa da 'yan jaridu.
A kwanannan ne dai aka ga hotunan jarumin da na jarumar suna yawo a kafafen sada zumunta na zamani wanda ke cewar wai jarumin ya auri jarumar a boye cikin sirri a Kano.
Ali Nuhun wanda shine mai kamfanin shirya finafinai na FKD, ya ce wasu mutane suna furta wasu kalamai ne ba tare da la'akari da irin matsalolin da za su janyo ba.
Jarumin ya kara da cewar shi wannan hoton da ake ta cece kuce akai hoto ne wanda aka dauka a wani shiri da ake kira da "Akushi" inda jarumar ta fito a matsayin matarsa a shirin.
Jarumin ya kara da cewar asalin fitar hoton har ya watsu a duniya shine a lokacin da aka daura shi a kafar sada zumunta kuma aka ba shi suna daga fim din Akushi.



No comments