Duk Dan Sandan Daya Sake Takurawa Yan Waya A Farm Center A Kano Asamai Ankwa A Kawo Minshi Abuja - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Duk Dan Sandan Daya Sake Takurawa Yan Waya A Farm Center A Kano Asamai Ankwa A Kawo Minshi Abuja



    'Duk Dan Sandan Da Ya Sake Musgunawa 'Yan Kasuwar Waya Ta Farm Center Dake Kano A Sanya Masa Ankwa A Kawo Min Shi Abuja'

    Babban sufetan 'yan sandan na kasa, Ibrahim K Idris ya bada umarnin gaggawa ga rundunar 'yan sandan jihar Kano domin su kamo wasu jami'an 'yan sanda da suke zalintar 'yan kasuwar saida waya ta Farm Centre ta hanyar karbar kudi a gurin su.

    Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin mataimakinsa na musamman akan kafafen yada labarai kuma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Magaji Musa Majia.

    Babban sufeton ya ce aka masu a matsayin masu laifi tare da sanya musu ankwa a aike da su ofis din shi dake garin Abuja domin yi musu hukuncin da ya dace da laifin da suka aikata.

    DSP Majia a cikin sanarwar yace, Ibrahim K Idris ba zai zuba ido yana gani a runga zalintar talakawa ta hanyar musguna musu da wasu 'yan sanda ke yi ba, shi ya sa ya dauki damara ta yaki da masu wannan halayya domin dawo da martabar aikin dan sanda a fadin kasar nan baki daya.

    No comments