Shugaban Kasan Nigeria Muhammad Buhari Ya Koma Ofishinsa Na Asali
Shugaban Kasa Buhari Ya Koma A Ofishinsa Na Asali.
A karshe Shugaba Muhammad Buhari ya koma
asalin ofishinsa wanda ya kauracewa tun bayan da
ya dawo jinya daga waje kuma ya kama aiki a ranar
19 ga watan Agusta.
An dai jima ana jita jitar cewa, Shugaban bai samu
sauki ba tun da aka samu rahotannin cewa daga
cikin gidansa yake aiki amma kuma daga baya
Kakakin Fadar Shugaban kasar ya yi karin haske kan
cewa ana gyaran ofishin ne sakamakon barnar da
beraye suka yi.
Sai dai kuma wasu majiyoyi sun
nuna cewa kauracewa ofishin na da alaka da
shawarwarin da aka ba Shugaban kan cewa an dasa
wani mugun abu a cikin ofishin.
Source By Rariya

No comments