Dalilin Da Yasa Nake Qalu Balantar Malam Nasiru El'rufa,i Tijjani Ramadan - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Dalilin Da Yasa Nake Qalu Balantar Malam Nasiru El'rufa,i Tijjani Ramadan

    Dalilin Da Ya Sa Nake Kalubalantar Gwamna El-
    Rufa’i, Inji Tijjani Ramalan
    Alhaji Tijjani Ramalan, gogaggen dan siyasa ne, har
    ila yau kuma Shugaban Kungiyar Masu Fafutukar
    Dawo Da Martabar Jihar Kaduna (Kaduna
    Restoration Group) a turance.

    A tattaunawarsa da
    Manema labarai a kaduna, ya yi fashin baki kan
    harkokin siyasay Kaduna da na Nijeriya baki daya.

    Ga yadda ta kasance.
    Ku ne kan gaba a lokacin yakin neman zaben
    Gwamna el-Rufai, yanzu kuma kun raba gari, shin
    me yake faruwa ne?
    Ina son na yi bayani a nan na kuma warware komai
    daki-daki, mu ba wai muna maida hanun agogo
    baya bane, ko kuma muna kokarin taka wa el-Rufa’I
    burki bane.

    Mambobin kungiyarmu da yawansu
    daga jami’iyyar APC suke, a yayin da wasu
    mambobin suka fito daga sauran jam’iyyun kasar
    nan, inda suka taimaka sosai wajen kawo wannan
    gwamnatin daga matakin jiha da kasa baki daya ta
    fuskoki da daman gaske kuwa.

    Babban manufarmu dai ita ce mu tabbatar da
    kyakyawan shugabanci.

    Don haka, mu bamu neman
    kawo wa Malam Nasiru el-Rufa’I cikas.

    Amma mun
    sani gwamnati dai ya ci rabin zango daga cikin
    shekarunta hudu da ke gabata, akwai bukatar mu
    bawa gwamna shawarori masu muhimmanci domin
    a samu nasara tafiyar da lamura yadda suka dace.

    Wannan dalilin ne ya sanya muka hada kanmu
    domin fitar da takardar manema labaru. Mun rubuta
    wasiku da dama zuwa ga gwamnan. Za kuma mu ci
    gaba da hakan, za mu kasance abokan gwamnan ta
    hanyar alkalaminmu.

    Domin muna son a samu
    shugabanci mai kyau kuma mai inganci a jihar
    Kaduna, don haka ne muke fadi tashin saita komai
    bisa daidai. Yanzu zan kasance abokin gwamnati ta
    hanyar ALKAMI.

    Me ya sa ka zabi zama abokin gwamna ta wannan
    hanyar maimakon tukararsa ka tsaye?
    Na kasance shugaban APC a Kaduna, na sani da
    yawan mambobin da suke tutiya da APC sun yi
    kaura ne daga jam’iyyun da suka hada da CPC.

    Na shiga jam’iyyar CPC ne bayan da na bar PDP, bayan
    da na iya fahimci PDP tana durkushewa.

    Da dama
    mutane sun shiga APC ne daga jam’iyyar PDP kai
    har da shi kansa el-Rufa’i.

    Maganar gaskiya ita ce dukkaninmu kowa ya yi
    kokari wajen tilastawa amsar karfin mulki daga
    hanun PDP daga matakin jihohi, kuma ba abun
    mamaki bane hakan.

    Na sadaukar da komai domin
    tabbatar da cewar mun kawar da PDP a jihar
    Kaduna.

    Domin da daman mu mun so hakan kuma
    mun yi nasarar fatattakar PDP a jihar nan.

    Na yi hidima sosai a APC, na kuma yi yaki sosai;
    na kuma rungumi kasada sosai.

    Ba zan taba
    mancewa ba; akwai gwamnan Kaduna da tsohon
    mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo wanda
    shi ma daga jihar Kaduna yake.

    Gaskiya na fuskanci
    kalubale da yawa.

    A takaice ma hatta gidan
    rediyona na Liberty ya gamu da suka kan cewar ina
    yi wa APC kamfe.

    Kuma har yau din ban yi nadamar
    tallata jami’iyyar da na yi ba, da kuma gagarumar
    gudunmawar da na bayar wajen yada manufar APC
    da kuma kawar da PDP.

    Babu wata dokar Nijeriya da ta haramta dukkanin
    gidan jarida ko gidan rediyo kada kuri’a ga
    jami’iyyun siyasa.

    Wannan dalilin ne ya sanya
    Liberty Radio da TB suka tsaya gami da bin bayan
    shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da Nasir el-
    Rufa’i.

    Gaskiyar magana mun tari aradu da ka.

    Da PDP ta
    yi nasara a zaben da aka fafata, Allah ne kadai ya
    san mene ne zai iya faruwa da mutane irina da suka
    yi tsayuwar daka don kawar da ita.

    Kowa ya san da
    wannan, na yi imanin da PDP ta yi nasara da ni kam
    sai na fuskacin barazana sosai, domin na yi hidima
    fiye da kima don kawo APC.

    Mun yi tsammanin
    Nasiru el-Rufa’i zai yi amfani da ikonsa wajen
    daukaka darajar jiharmu gami da kaita babban
    mataki, amma kuma sai muka ga yana sauka daga
    kan tsari, yana biye wa masu dora shi a keken bera.

    Yau shekara biyu da hawan wannan gwamnati, shin
    ra’ayinka a kanta ya canja ne?
    Shekaru biyu sun gabata a mulkinsa, muna kokarin
    ba shi shawarori ga-mu-ga-ga-shi, akwai wandanda
    muka rigaya muka yi masa, ta hanyoyin rubuta
    takarda da sauransu.

    A matsayina na shugaban kungiyar da ke fafatukar
    farfado da jihar Kaduna, ina da alaka ta kai tsaye
    da gwamna.

    Ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba,
    na sha jawo hankalin gwamnan Kaduna dangane da
    nade-naden mukamai, na ke ce masa ba fa zai
    tsaya yin amfani da zallar ‘yan APC bane, dole ne
    ya duba sauran jam’iyyun domin akwai wadanda
    suka yi masa hidima har ya zama gwamna.

    Na bashi shawara kada ya kuskura ya tsuke hannunsa
    wajen zallar APC ya yi kokari ya surka da sautan
    mutunen jam’iyyun siyasan.

    Domin ina da ilimin
    siyasa jiya da yau, na kuma san abubuwan da suka
    dace a siyasance.

    Na kasance dan siyasa yau sama da shekaru 30,
    akalla ina da ilimi kuma na dauki darussa sosai
    daga wasu.

    Na fara harkar siyasa ne tun a 1983 a
    karkashin jam’iyyar (NPN).

    Na taba zama wakili na
    musamman ga gwamnan jihar Ribas marigayi Chief
    Melford Okilo a jihohin Arewa.

    Wanda ofishina ke
    jihar Kaduna.

    Bayan nan kuma, na zo na kasance
    shugaban (NRC), kafin hakan na zama mamba a
    kwamitin (NRC) da dai sauransu.

    Source By Rariya

    No comments