Matashin Daya Fallasa Kudaden Dake Gidan Ikoyi Ya Zama Maloniya - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Matashin Daya Fallasa Kudaden Dake Gidan Ikoyi Ya Zama Maloniya


    Matashin Da Ya Fallasa Kudaden Gidan Ikoyi Ya
    Zama Miloniya - Magu.

    Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya tabbatar
    da cewa matashin da ya fallasa inda aka boye
    makudan kudaden nan na Dala milyan 43.4 a wani
    gida da ke yankin Ikoyi a jihar Legas a halin yanzu
    ya zama Miloniya.

    A bisa sabon salon yaki da rashawa, duk wanda ya
    taimaka aka gano kudaden sata na gwamnati, za a
    ba shi kashi 2.5 na yawan kudaden.

    A cewar
    Shugaban EFCC, a halin yanzu ana ci gaba da ba
    matashin horo na musamman kan yadda zai sarrafa
    kudaden saboda bai taba ganin irin wadannan
    kudade a rayuwarsa ba.

    Source By Rariya

    No comments