Shugaban Kasa Muhammad Buhari Ya Amince A Biya Kudin Makarantar Yan Matan Chibok - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Shugaban Kasa Muhammad Buhari Ya Amince A Biya Kudin Makarantar Yan Matan Chibok


    Buhari Ya Amince A Biya Kudin Makaranta 'Yan Matan Chibok Da Ke Karatu Jami'ar Atiku.

    Shugaba Muhammad Buhari ya amince a biya sama da Naira milyan 164 na kudaden makarantar 'yan Matan Chibok su 106 da ke karatu a jami'ar ' American University of Nigeria, (AUN)' da ke Yola mallakar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

    Shugaba Buhari ya amince da biyan kudaden ne a lokacin da ya karbi rahoton yadda aka gyara halayen 'yan Matan kafin su shiga jami'ar. Haka ma, Buhari ya jaddada manufarsa na ganin an ceto sauran 'yan Matan Chibok din wadanda har yanzu ke hannun mayakan Boko Haram.

    No comments