Dole Ne Atiku Ya Roki Obasanjo Gafara Cewar Jonathan - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Dole Ne Atiku Ya Roki Obasanjo Gafara Cewar Jonathan



    Dole Atiku Ya Roki Obasonjo Gafara Kafin PDP Ta Karbe Shi - Jonathan.

    A yayin da ake hasashen Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar zai koma PDP bayan ficewarsa daga APC, Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya ce dole sai Atiku ya roki Cif Olusegun Obasonjo kafin jam'iyyar PDP ta amince ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar.


    Wannan ikirari na Jonathan yana daga cikin yarjejeniyar da Atiku ya kulla da jiga-jig an jam'iyyar PDP kafin ya fice daga APC duk da yake ya taba yin alkawarin cewa ba zai taba barin jam'iyyar ba. A shekaranjiya Juma'a ne dai, Atiku Abubakar ya bayar da sanarwar ficewa daga APC bisa dalilin cewa jam'iyyar ta yi watsi da matasa.

    No comments