Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abukakar Ya Amince Ya Bawa Obasanjo Hakuri - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abukakar Ya Amince Ya Bawa Obasanjo Hakuri



    Atiku Ya Amince Ya Roki Gafarar Obasonjo Don Samun Karbuwa A PDP.

    Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya karbi shawarar Goodluck Jonathan inda ya amince ya sadu da tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo don neman gafararsa saboda ya samu karbuwa a cikin jam'iyyar PDP inda yake son tsayawa takarar Shugaban kasa.

    Mai Magana da Yawun tsohon Shugaban kasar, Mista Mazi Paul ya ce Atiku zai tafiya tare da kowa ne don haka zai sadu da Cif Obasonjo don ganin ya samu kaiwa ga bukatarsa ta siyasa. Cif Obasonjo dai ya yi alwashin cewa idan har yana raye zai tabbatar da cewa Atiku Abubakar bai zama Shugaban kasar Nijeriya ba.

    No comments