Nazir M Ahmad (Sarki Waka) Sai An Biyani Diyyan Naira Millions Dari Sakamakon Amfani Da Wakata Ba Tare Da Izini Na Ba
Sai An Biya Ni Diyyar Naira Milyan Dari Kan Amfani
Da Wakata Da Aka Yi Ba Da Izinina Ba, Inji Nazir M.
Ahmad
Shahararren mamawakin Hausan nan Naziru M.
Ahmad wanda aka fi sani Da Sarkin Waka ya nemi
diyyar naira milyan dari daga wajen Ebonylife
T.V.sakamakon yin amfani da wakar sa da suka yi
a fim din su ba tare da izininsa ba.
Ga cikkakiyar hirarsa da Usman Mu'azu kan lamarin.
Da farko zamuso ka gabatar da sunanka?
Sunana Naziru M. Ahmad (Sarkin Waka).
Mun samu labari akwai wani gidan talabijin da yake
amfani da wata waka taka ko za ka fada mana
wace waka ce?
Eh, sunan wakar bincike, muna ce mata bincike.
Mun samu labarin suna amfani da wannan wakar
bada izininka ba haka ne ko yaya abin yake?
Hakane suna amfani da ita bada izinina ba kuma
mun nemi su fada mana dalili sun yi shiru, shine
muka ce za mu bi hanyar da ta dace domin karbar
hakkinmu.
Ta wace hanya kuka yi kokarin sanar da su?
Mun bi ta hanyar lauyan mu domin ya tura musu a
rubuce, kuma ya yi hakan amma ba su ce komai
ba.
To amma bayan wannan matakin wane irin mataki
nan gaba kuke ganin za ku dauka?
Eh, mataki na gaba shine za mu sake tura musu
kamar yadda muka yi a baya, amma idan ba su ce
komai ba zamu bi wata hanyar da ta dace ta kotu
domin idan suna ganin sun fi karfin mu to ba su fi
karfin doka ba.
Malam Nazir mai karatu zai so ya ji wai shin ta ina
suke amfani da wannan wakar taka?
Suna amfani da ita ne ta hanyar sa ta a cikin wani
'Series' dinsu mai suna 'SON OF THE CALIPHATE'
Season 1.
Sun sa ta ne a matsayin kidan taushi na fim din
wato 'sound track', saboda sun raina mu, shine
muke ganin bai kamata su ci bulus ba, idan sun
saba yi wa wasu haka su share to mu ba za mu bari
ba.
Idan na fahimce ka wannan dalilin ne ya sa kake
neman hakinka a gunsu?
E wannan shine dalili, saboda su yi min bayani wa
ya ba su kaya na ba da izini na ba.
To kai yanzu kana da hujjojin da za su tabbatar da
wannan abin da kake zargi?
Kwarai kuwa.
Kamar me dame ka tanada da za ka gabatarwa kotu
idan ta bukaci hakan?
Akwai hotuna da datas na mintuna da lambar
season din da lambar 'episode' din da aka yi
amfani da kayan nawa.
Dama a doka idan aka yi amfani da kayanku irin
haka wace hanya ake bi dan ganin an warware
matsalar, ta yaya za’a warware matsalar?
Diyya za su biyani na amfani da kayana ba tare da
na sani ba, tun da doka ta ba ni dama na yi hakan.
Akwai abinda ka kiyasta za su baka ne?
E munyi magana da lauyoyi na sun ce a yi musu
saukin rangwame su biya naira miliyan dari kawai,
saboda a gargade su dan gaba kar su kara taba
min kayana.
Ba za ka yi musu sauki ba saboda ganin cewa
kamar kudin sun musu yawa?
Kai ne suka yi wa yawa, ni a guri na ma ban samu
yadda nake so ba, na yi musu haka ne saboda
shine na farko da suka yi min, kuma tunda ka ga
sun dauka abin ne ya yi musu kyau tunda ba za su
dauki abinda zai lalata musu aiki ba, to sun yadda
na sha wahala wajen yin wakar ne shi ya sa bai
kamata ya yi kasa da haka ba.
Baka ganin cewa sakaci da kuke nunawa game da
kayanku ne ya bada dama suka yi muku wannan
abin?
A’a ni ba na sakaci da kayana tunda duk abinda
nake yi da ya shafi fasaha ta ina masa copy right ka
ga ba za ka ce na yi sakaci ba.
Yanzu ka kai kara kotu ne ko dai za ka kai nan
gaba?
Ai tuni maganar tana kotu, muna jiran lokaci ne
kawai.
A karshe wani irin kira ko shawara za ka baiwa
abokan sana’arka game da irin wadannan
matsalolin?
Shawarar da zan ba su ita ce su dinga kula da duk
abinda ya shafe su suke da hakkin mallakar sa,
domin kare mutuncin hakkin kayansu.
Mun gode.
Nima nagode.






No comments