Jarumawan Kannywood Goma Da Suka Fi Kudi A Masana,antar Fina-Finan Hausa
JARUMAN KANNYWOOD 10 DA SU KA FI ARZIKI.
Akwai dumbin jarumai da su ke da kudi a
masana'antar kannywood sai dai mun duba mutane
10 da Su ka fi kudi a wannan shekara bisa dogaro
da dalilai na zahiri.
1. Ali Nuhu shi ne jarumin da ya fi kudi a
kannywood, Ya na da gida a kano da hotal a bauchi
, ya na yiwa kamfanoni kimanin shida ko bakwai
jakadanci Ya kai kimanin shekaru 15 ya na jan zare
a matsayin jarumin jarumai a kannywood.
2. Adam A. Zango shi ne jarumi na biyu da ya fi
kudi a taurarin kannywood, Ya kammala gina wani
kasurgumin gida a kaduna , Ya na karbar miliyan
daya da rabi idan an gayyace shi biki kuma akalla
ya kan ziyarci irin bukukuwan sau uku a wata daya,
sannan ya na karbar kimanim dubu dari uku kafin ya
fito a fim kafin daga bisani ya daga zuwa dubu dari
biyar , ya kan yi fina finai akalla hudu a wata daya,
sannan shi jakadan kamfanin MTN ne a kowanne
wata ya kan samu kudi daidai da kimar naira
miliyan biyar.
3. Dauda Kahutu Rarara ya shiga jeri na uku cikin
ma Su kudin kannywood , tun bayan zaben dabya
gabata , Ya na da wani makeken Gida a zoo road
kano.
4. Mawaki Nura M. Inuwa shine na hudu a lissafin
wanda su ka fi kudi a kannywood , ya na fitar da
albam biyu duk shekara, wanda su ke samar da
kimanin miliyan 25, Ya kasance ya fi karkata a
wakokin biki wadda bayanai sun nuna ya na karban
dubu dari biyu da hamsin a kowacce waka, sannan
a mako daya ya kan yi akalla wakoki biyar.
5. Halima Atete ita ce ta biyar a jerin wanda su Ka
fi kudi a kannywood kuma ta farko a jarumai mata,
ta dauki tsawon lokaci ta na shirya fina finai da
kudinta.
6. Sani danja shine na shida a rukunin attajiran
kannywood ya na da Gida a abuja, Ya samu
makudan kudade a lokacin zaben 2011 inda ya rika
taya shugaban kasa kampe a wanchan lokaci.
7. Sadik Sani Sadik shine na bakwai a jerin Wanda
su Ka fi kudi a taurarin kannywood.
8. Nafisa Abdullahi ita ce ta takwas a cikin jerin
attajiran kannywood kuma ta biyu a cikin mata, Ta
na shirya fim na kashin kanta.
9. Hadiza Gabon ita ce ta tara a rukunin attajiran
kannywood .
10. Aisha Aliyu Tsamiya ce ta goma a rukunin
taurarin attajiran kannywood.

No comments