Anbude Sabon Gidan Cin Abinci Tsirara A Kasar Faransa - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Anbude Sabon Gidan Cin Abinci Tsirara A Kasar Faransa


    Subuhanallahi.
    Innalillahi wainna ilaihi raji'un.
    Alumma Wannan duniyar fa tazo karshe.

    A Faransa An Bude Sabon Gidan Abinci Da
    Mutane Zasu Dinga Zuwa Zigidir
    A kasar Faransa an bude wani sabon gidan
    abinci da mutane zasu dinga zuwa cin abinci
    zigidir.

    Sabon gidan abinci mai suna O’naturel
    an bude shi ne a babban birnin kasar Faris,
    sabon gidan abincin zai baiwa dangi da iyalai
    damar zuwa su yi karin kumallo ko cin abincin
    rana ko cin abin dare.

    An dai bude wannan sabon gidan abincin ne a
    ranar Juma’ar nan da ta gabata, bayan da masu
    rajin yawo tsirara sukai ta kiraye kirayen a bude
    shi, domin suje su gwangwaje tare da iyalansu.

    Manajan gidan sabon abincin Mista Stephane
    Saada, ya bayyana jin dadin kan irin yadda
    jama’a ke tururwa zigidir suna zuwa domin su ci
    abinci a wajensu.

    Yace wannan abin da mutane
    ke yi ya kara musu kwarin guiwa, kuma zasu
    zage dantse wajen ganin sun hidimtawa
    mutane.

    Haka nan, suma masu makwabtaka da gidan
    abincin sun nuna jin dadinsu kan yadda aka
    bude sabon gidan abincin da zai basu damar
    zuwa cin abinci da iyalansu zigidir.

    A wannan gidan abinci, kudin abinci mafi arha
    shine wanda kudinsa ya kama kudin tarayyar
    turai (Euro 30) Kimanin Naira 12,420. Jama’a
    da dama sun bayyana farashin da cewar bai yi
    tsada ba.

    Allah daya gari bamban.
    ALLAH KASA MU CIKA DA KALMAR (LÃILAHA
    ILLALLAHU MUHAMMAD RASULILLAHI).

    No comments