Kungiyan Kiritocin Nigeria Ta Nemi Nigeria Ta Fice Daga Dukkan Wata Kungiya Ta Muslunci
Kungiyar Kiristoci Ta Nemi Nijeriya Ta Fice Daga
Kungiyoyin Musulunci.
Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya ( CAN) ta yi kira ga
majalisar dokokin Nijeriya kan ta cire Nijeriya daga
dukkan kungiyoyin kasa da kasa da ke da alaka da
addinin Musulunci.
A wani taro da kungiyar ta yi Legas ta zargi
shugabannin kasa na da da na yanzu da yunkurin
mayar da Nijeriya kasar Musulunci inda ta nuna
cewa akwai wani tanadi na wata kungiyar Musulunci
da Nijeriya ke ciki wanda ya nemi kawo karshen
duk wani tsari da ya jibinci Turai.

No comments