Gwamnatin Shugaban Kasan Muhammad Buhari Zata Samarwa Matasa Sama Da Milliyon 15 Aikinyi
Matasa Milyan 15 Za Su Samu Aikin Yi A
Gwamnatin Tarayya
Daga Sheriff Sidi
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar matasa
milyan 15 za za su samu aikin yi a kokarin da take
yi na bunkasa tattalin arziki.
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba
Muhammadu Buhari kan Shirin Bunkasa Tattalin
Arziki (Economic Recovery Development Plan)
Malam Sani Yakubu ne ya bayyana hakan a wajen
bude babban taron Majalisar Koli ta Harkokin
Kasuwanci, Masana'antu da Saka Jari kashi na tara
a yau Laraba a otel din Giginya da ke Sakkwato.
"Babbar manufa ita ce samun nasara a tattalin arziki
ta hanyar raguwar hauhawar farashi, tsayayyen
farashin musayar kudi da samar da hanyoyi ga 'yan
Nijeriya domin su shiga harkokin kasuwanci." Ya
bayyana.
Yakubu ya kuma bayyana cewar a karkashin shirin
al'ummar Nijeriya za su ci gajiya a lamurran
makamashi da sha'anin wuta da man fetur tare da
bunkasa sufuri.
Ya ce ba abin mamaki ba ne yadda Kasuwanci,
Masana'antu da Saka Jari ya zama daya daga cikin
fannoni biyar da aka baiwa muhimmanci domin fita
daga matsin tavarvarewar tattalin arziki a Nijeriya.
A jawabinsa Babban Sakataren Ma'aikatar
Kasuwanci, Masana'antu da Saka Jari ta Kasa, Mista
Edet Sunday Akpan ya bayyana cewar a baya-bayan
nan Tattalin Arzikin Nijeriya ya fuskanci kalubale
sosai musamman ta dalilin tabarbarewar Tattalin
Arzikin Duniya bakidaya a bisa ga dogara kacokam
kan man fetur.
Akpan ya bayyana cewar a yanzu haka Nijeriya ta
fita daga kangin tabarbarewar tattalin arziki da kashi
0.55% wanda kuma yake karuwa.

No comments