Gaskiya Ta Fara Bayyana Game Da Kisan Da Akayiwa Fulani Numan Dake Jihar Adamawa - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Gaskiya Ta Fara Bayyana Game Da Kisan Da Akayiwa Fulani Numan Dake Jihar Adamawa



    RAHOTO NA MUSAMMAN AKAN KISAN FULANI A ADAMAWA

    *Abokan Zaman Mu Bachama Muke Zargi

    *Gwamna Bindow Ya Bada Tallafin N500,000 Ga Marasa Lafiya

    DAGA MAHMUD ISA YOLA

    Ranar talatar da ta gabata ne jihar Adamawa ta wayi gari da tagwayen labarun tashin hankali, na fashewar Bomb a Mubi da kuma kisan kare dangi da aka yi wa kabilar Fulani mazauna karamar hukumar Numan.

    Sama da gawaki 55 ne aka samu yayin da har yanzu ake kan samun wasu, kana kuma sama da mutum 40 ne suka samu rauni bayan harin da wasu da ake zargin ‘yan kabilar Bachama ne suka kai kan kauyen Fulani na Shelewol dake cikin karamar hukumar ta Numan.

    Karamar hukumar Numan dai daya ne daga cikin manyan kananan hukumomin jihar Adamawa inda mafiya yawan mazauna garin kabilar Bachama ne. wannan yasa masarautar Numan din ta zama tushen kabilar ta Bachama. Duk da haka, akwai daidaikun kauyuka a cikin garin na Numan wadanda Fulani ke zama tun shekaru da dama da suka gabata. Amma fulanin sune mafi karanci a cikin yawan  mutanen garin.

    Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai hari kan Fulanin ne da misalin karfe uku zuwa hudu na yammacin ranar litinin da ta gabata. Maharan sun biyo mata da yara da suke dawo wa daga kiwo inda suka far musu tun a kan hanya kuma suka bi su har matsugunan su suna kashewa.

    Wakilin jaridar Rariya Mahmud Isa Yola da ya ziyarci yankin da abun ya faru ya tattauna da Ardo (shugaban Fulanin da aka kai wa hari) inda ya bayyana  ta’adin da aka yi musu a matsayin abun da basu taba ganin irin shi ba. ‘Ardon’ mai suna Alh Isyaku Galadima ya jaddada cewa babu wadanda suke zargi da wannan mummunan aiki sama da ‘yan kabilar Bachama da suke kewaye da su.

    Yace “Dama muna zuwa yankin Demsa yin abunda mu Fulani muke kira da shekara. To bayan da muka dawo zuwa asalin garin da muke zama Shelewol a Numan, sai muka sanar da Hakimin Numan cewa mun dawo. Muna zaune lafiya sai yaran mu suka tsallake kogi, to kogin nan munyi sharadi cewa mu ba zamu tsallake shi mu shiga yankin Bachama ba. Sai Hakimi ya kira ni yace min to tunda haka ya faru sai mu tattara mu bar wurin, ko mu koma inda muke zuwa shekara.

    “Ni kuma nace mishi maganan tashi kam bata taso ba, tunda mun jima muna zama a wannan yanki, amma ina bada hakuri akan laifin da aka yi. Kuma ina goyan bayan a hukunta yaran da suka yi wannan laifi. To bayan nan sai mai jimillar yankin mu wanda Bachama ke kira ‘Zumotokiken’ ya aiko a gaya mana cewa in ba mu bi umurnin hakimi muka tashi ba zai aiko mana da yaran sa. Mu kuma bamu ce komai ba.

    “kwatsam ranar litinin da yamma ina cikin garin Numan sai labari ya riske ni cewa yanzu haka ana kashe mana mata da yara da suke dawowa daga kiwo”. Inji Ardo Isyaku.

    Da wakilin RARIYA ya tambaye shi ko akwai wani sa’insa da ya sani tsakanin su da kabilar Bachama Ardon yace babu abun da ya sani, illa cewa Zumoto Kiken din ya taba yin sarauta a baya aka sauke shi, inda a sarautar da yayi a bayan ya taba zuwa da matasa rugan Fulani yasa aka yi ta tone tone yana ikirarin zargin su da boye makamai.

    Duk wani yunkuri na jin ta bakin Zumotokiken din ya gagara a lokacin hada wannan rahoto sakamakon rashin samun sa a waya.

    Daga Bisani Ardo Isyaku ya zaga da wakilin RARIYA asibitin kwararru dake Yola, don nuna ma sa wadanda suka samu raunuka.

    Galibi wadanda suke kwance a asibitin mata ne da kananan yara wadanda suka samu munanan raunuka daga sarar adda, mashi da kuma harbin bindiga. Takaddun asibiti da RARIYA ta samu sun nuna cewa mutane talatin da biyu ne ke kwance a asibitin na Yola. 30 daga cikin su sun samu raunuka daga sarar adda, yayin da daya kuma mai suna Malam Husaini ya samu raunin harbin bindiga kirar AK 47, wata yarinya mace kuma mai shekaru 14 ta samu raunuka daga sukan mashi da harbin bindiga.

    Aisha Alh Kawu, uwa ce ga jaririya Hassana ‘yar kwana uku a duniya wacce aka kashe a harin. Aisha ta bayyana wa wakilin mu yanda aka kashe ‘yar ta a idon ta: “Sun zo suna kisa ba ji ba gani, suka kwace yarinya, daya ya burma mata mashi a ciki, daya kuma ya raba k*nta biyu da sarar adda!”

    Ita ma Hafsat Alh Ade tace kisan da aka yi abu ne da baza su taba mantawa ba a tarihi. Hapsat ‘yar shekaru 32 tace zaluncin da aka yi musu, Allah ne kadai zai mu su sakayya.

    Abubakar A. Buba, mazaunin Yola ne da yake lura da marasa lafiya da ake shigowa da su asibitin daga inda fitinan ya faru, ya bayyana wa wakilin mu cewa kashi 47 na wadanda suke kwance a asibitin yara ne, yayin da kashi 50 kuma suke matan aure da ma wadanda basu yi auren ba.

    Da yake bayani akan yanda marasa lafiyar suke jinya Buba yace: “zan fara da godiya ga kungiyoyin addinai irin su ‘yan agajin Izala, Fityanul Islam, kungiyan mata na Nisa’us Sunnah da dai sauran su wadanda suke tare da mu tun faruwar wannan abu zuwa yanzu. Ita gwamnati, agajin da ta yi mana a nan ba zamu yaba ba, ba kuma zamu kushe ba. Amma gwamnati ta sani, ita ce alhakin lafiyan wadannan yake a hannun ta. Kamar yanda alhakin tsare lafiyar su yake a hannun ta.”

    Bayanai sun yi nuni da cewa, maharani sun kwashe dabbobin Fulanin da dama, inda wasu kuma suka kashe su.

    Gwamnan jihar Adamawa sanata Umar Jibrilla Bindow ya ziyarci asibitin inda ya bada tallafin Naira dubu dari-biyar (N500,000) ga wadanda suke jinya a asibitin.

    Zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, kakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a hirar da yayi da gidan Radio BBC ya bayyana cewa ba su kama wani da yake da hannu cikin kai harin ba tukunna. Amma dai yayi kira ga mazauna garin na Numan su bawa jami’an tsaro hadinkai yayin da take binciken lamarin, kana kuma a zauna lafiya ta hanyar mutunta doka da oda.

    Source By Rariya

    No comments