Kalamai Masu Ratsa Zuciya Daga Wani Abokin Billiyaminu Wanda Matarsa Ta Kasheshi - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Kalamai Masu Ratsa Zuciya Daga Wani Abokin Billiyaminu Wanda Matarsa Ta Kasheshi


    "Mun Hana Bilya Auren Maryam Ya Ki Sauraron Shawarar Mu"

    *Kalaman Juyayi Daga Abokinsa Mustapha Dikko

    YAU Ya Kamata Na Kira Ka Na Yi Maka Murnar Cika Shekaru 36 A Duniya Sai Ga Shi Ba Ka Tare Da Mu. atukar Kokari Hana Hawayen Jimami Zuba Daga Idanuwana A Yayin Da Na Ke Tunanin Ka,  Na Ke Kuma Tunanin Rayuwa Babu Bilya. Ina Cike Da Tsananin Alhini Ina Kuma Nadamar Kyale Ka Da Muka Yi Ka Auri Maryam.

    Na So Ace Na Ci-gaba Da Dagewa Wajen Hana Ka Aurenta, Na Yi Iya Bakin Kokarina Amma Ina Ma Na Matsa Fiye Da Yadda Na Yi. Na Ji Matukar Haushinka Da Ka Dage Sai Ka Aure Ta, Don Haka Muka Watse Muka Kyale Ka Da Wannan Mashekiyar.

    Da Farko Ta Raba Ka Da Masoyiyar Matarka, Sannan Ta Raba Ka Da Danginka Da Kuma Abokanka. Ya Bilya Ina Takaicin Rabuwa Da Kai Yau Maryam Ta Raba Ka Da Wannan Duniya Har Abada. Ba Na Manta Abinda Kake Cewa, Yayin Da Kake Raye:

    "Idan Na Yi Aure Zan Sallama Kaina Kacokam Ga Matata, Ba Na Son Fitinar Mata, Kawai A Zauna Cikin Aminci". Da Gaske Ka Nemi A Zauna Cikin Aminci Ita Kuma Ta Yi Amfani Da Wannan Damar..

    No comments