Jarumin Kannywood Ya Zama Jakadan Majalisar Dinkin Duniya
Sani Danja ya samun sabon mukami a majalisar
dinkin duniya inda aka nada shi a matsayin
jakada a fannin kafa manufa ta samun cigaban
zamani (SDGs) ta majalisar.
Anyi taron kaddamar da jarumai a garin Abuja
ranar laraba 25 ga watan octoba yayin da ake bikin
nuna farin ciki zagoyowar ranar majalisar dinkin
duniya.
Danja wanda aka fi sani da 'sarkin nishadi na
arewa' ya shahara a fadin Nijeriya bisa ga rawan
da yake taka wa a harkar nishadantarwa.
Wannan sabon daukaka yana cikin jerin jakadanci
da ya samu daga kamfanin Glo, Rotary, gidauniyar
save the children, western loto da sauran su.
Banda Sani Danja sauran jaruman kannywood da
suka samu mukamin jakadanci na majalisar dinkin
duniya akwai Yakubu Muhammed da Uzee Usman.
A cikin manyan baki da suka halarci taron akwai
Ministan wassannin da ayyukan matasa Solomon
Dalung da babban mataimakin shugaban kasa a
kan SDGs Princess Adejoke Orelope Ade Fulure.
Sauran jaruman Nijeriya da suka samu matsayin
sun hada da mawaki Tuface, Sunny Ade, Omotola
jalade Ekehinde, Chigurl, Teju babyface, Alibaba
da Zdon Paporella .




No comments