Shahararren Mawakin Hausa Sa'eed Nagudu Zai Angwance Ranar Juma,a
Mawaki Sa'eed Nagudu Zai Angwance
Ga yadda za a gudanar da shagulgulan bikin; KAMU ranar Alhamis da misalin karfe 3:00pm a New Era Cinema
Arabian Night shi ma a ranar Alhamis da misalin karfe 8:00pm a Mufees Garden Filin Sukuwa Jos.
Sai kuma daurin aure a ranar Juma'a (15/09/2018) da misalin karfe 2:00pm a Layin Dankarfalla Jos.
Jim kadan bayan addu'ar daurin aure kuma, sai a gudanar da Ranar 'yan fim da misalin karfe 4:00pm a Mega Park Ring Road Jos.
Washegari Asabar kuma za a buga wasan kwallon kafa a makarantar GSSS Gangare Jos da misalin karfe 4:00pm.
Sai kuma dina a Plateau Hotel Jos da misalin karfe 8:00pm shi ma a ranar Asabar.








No comments