Jarumar Kannywood Rashida Sa,a Tayi Allah Wadai Da Kisan Da Akewa Musulmai A Kasar Myanmar - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Jarumar Kannywood Rashida Sa,a Tayi Allah Wadai Da Kisan Da Akewa Musulmai A Kasar Myanmar

    Allah Wadarai Da Kasashen Da Suka Yi Shiru Da
    Halin Ko In Kula Kan Musulman Burma, Cewar
    Rashida Mai Sa'a.

    Fitacciyar Jarumar Fina-Finan Hausa Rashida
    Adamu (Rashida Mai Sa'a) ta yi "Allah wadarai da
    halin ko in kula da wasu Gwamnatocin kasashen
    Musulmai sukeyi dangane da Abubuwan da suke
    faruwa a Burma/Rohingya.

    Yakamata su dauki
    matakin dazai kawo karshen zuwan wannan
    Al'amarin a nan gaba"
    "Idan za ku iya tuna abinda ya faru, a cikin watan
    Yuni na shekarar da ta gabata ne wani musulmi dan
    kasar Amurka mai suna Omar Mateen ya kai wani
    farmaki a wani gidan rawa inda yan luwadi suke
    taruwa suna rawa tare da badala a garin Orlando na
    Cikin kasar America.

    Cikin Ikon Allah ya kashe
    sama da mutane 50 daga cikin su".

    "Idan har mai karatu zai iya tunawa a lokachin ne
    shugabanin kasashen duniya cikin gaggawa ba tare
    da yin wani jinkiri ba suka aika sakon jaje zuwa ga
    kasar Amurka har ma suke bayyana hakan a
    matsayin mummunan aikin ta'addanchi tare da yin
    tir da kuma Allah wadai ga haka.

    "Tun a cikin shekaru fiye da 200 da suka wuce,
    akwai Musulmai a yankin Arakaan wanda adadinsu
    ya haura kimanin milyan 3 ko 4 a yayin da mabiya
    addinin Buddah adadin su ya kai su milyan 50, an
    kone musu gidajen musulmai masu dimbin yawa,
    an kuma yi wa malaman su kisan wulakanci.

    Da yawa daga cikin su sun bar gidajen su, wasu a
    hanyar ceton rayukan wasu, sun rasa nasu rayukan,
    amma sai a yanzu ne abubuwan suke kara fitowa
    fili.

    "Shin amma me ya sa har yanzu shugabannin
    kasashen duniya ba su furta komai dangane da irin
    kisan kiyashin da ake yi wa Musulman Burma/
    Rohingya ba?
    "Amma kuma sun yi saurin aikawa da sakon jaje
    dangane da abinda Omar Matee ya aikata.

    "Shin su ba Musulmai bane? Ko su an mayar dasu
    saniyar ware ne?
    "Duk Musulmin dan Uwan Musulmi ne.

    Ya kamata a ce irin wadannan tambayoyi suna yin
    shawagi a cikin kwakwalwar mu"

    No comments