Masarautar Kano Bata Na korade Bello A Matsayi Sarkin Mawaka Ba
Masarautar Kano Ba Ta Nada Korade Bello sarautar
"Sarkin Waka Ba".
Ya kamata makiya su sani cewa duk irin kulle-
kullensu ba za su iya kayyade hukuncin Allah ba
akan Sarkin Kano.
Kwanaki haka aka yi ta yad'a jita-jitar wai za a nada
sabon Danmasani domin tayar da zaune tsaye wasu
'yan bani-na'iya su kayi ta zage-zage ba gaira ba
dalili.
Tabbas Korade Bello ya zo Kano yayi hawa ya
sauka ya gaida Sarki wannan girmamawa ce kawai,
in sarki nason ya yi masa nadi ai ko wacce
masarauta tana da ikon nad'a ko wacce Kabila
nadin da ta ke so, amman ba a d'aka ake yin nad'in
ba, a bainar jama'a ake yi, shin a ina aka taru aka
nada Korade dinne?
Ina mamakin wasu mutane Wallahi, mun taso mun
ga (Garsam)Fernandez cikin hakiman Kano, a
idanunmu an bawa Wazirin Jama'a sarauta mai
girma a middle belt daga k'abilar Tibi.
An bawa
Mallam Shekarau sarauta a Enugu da Nsuka, an
bawa su Atiku Abubakar da sauransu.
Ko watannin
da suka shude sarautu biyu aka nad'a Farfesa
Abdallah Uba Adamu a garuruwan inyamurai kuma
d'ane cikakke a masarautar Kano a tarihi ma yana
cikin magada gadon sarautar amma a Kudu aka fara
ba shi sarautun kafin ya samu ta gida.
A cikin
mashahuran attajiran kasar nan da akwai da yawa
masu sarauta a Kudu don haka kar ayi mamakin
gani a Arewa.
Har wani darektan Fim zai iya fitowa ya bugi kirji
yayi wani sharhi ga Sarki mara tushe yakamata dai
a yi hattara a fara sanin tushen zance a tabbatar da
shi kafin fitowa kafafen sadarwa don yad'a shi.
Ga duk wanda ya san al'adu na neman sarauta a
masarautar Kano yasan yadda ake nemanta kamar
auren budurwa da nasaba da cancanta da isa da
biyayya da asali da gado da kaunar sarautar, ba wai
kawai kiran mutum ake a ce jeka wane an baka
sarauta ba, bisa al'ada ko ka gada nema kake
kuma ka nuna soyayyarka a fili, ko ka tura wakilai
wajen Sarki a nema maka ko kuma in wani naka
yana gadon wata sarauta ya mutu a baka gadonsa
inta fad'o kanka shikenan.
Masu cewa a ba wa Naziru Sarkin Waka lallai ya
kamata su sani cewa sarauta daban take da kusanci
ko alaka.
Sarkin tabshi da Jankidi sun kwashe lokaci suna yi
wa marigayi Sarkin Kano Halifa waka amma ba a yi
musu Sarkin Waka ba.
Aminu Ala ya shafe shekaru yana yi wa marigayi
Sarkin Kano Ado Waka Allah Ya ji kansa amma bai
nada shi Sarkin Waka ba ba wai don bai cancanta
ba a'ah domin matakan neman sarauta ba a
bayarwa sai an nema.
Kamar neman aure ne sai ka gani ka ce kana so,
sannan ka tura manya tare da bin duk wata hanyar
da ka san za ka bi in Allah Ya sa kana da rabo ace
an baka in baka da rabo ace maka an ba wa
waninka.
Korade Bello yana nan a Koradensa ba Sarkin waka
ba, ba'a ayyana ba shi nad'i ba wannan shaci-fadi
ne kawai na marasa aikin yi.
Allah ya taimaki Sarki Sanusi II ya kara masa
martaba.





No comments