Fitacciyan Jarumar Kanywood Ta Fara Fitowa A Fina-Finan Nollywood - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Fitacciyan Jarumar Kanywood Ta Fara Fitowa A Fina-Finan Nollywood

    Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.
    Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta fara gwada sa'arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a bangarori daban-daban.
    A cewarta, "Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood. 
    "Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna 'Lagos real fake life". 
    "Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin 'yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim". 


    Image captionHadiza Gabon ta ce ta fito ne a matsayin 'yar arewa

    Hadiza Gabon ta kara da cewa "Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al'adata ba".
    Jarumar ta ce babu wani "bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadin soma fitowa a fina-finan Nollywood". 

    Source By Bbchausa

    No comments