Sojoji Mata Sun Fara Kokawa Bisa Rashin Samun Mazajen Aure - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Sojoji Mata Sun Fara Kokawa Bisa Rashin Samun Mazajen Aure

    Babu Wanda Ya Ke Son Aurenmu- Macen Soja.

    Sojoji Mata na Najeriya sun zargi maza da tsoron
    kakin soji wanda shine dalilin da ya sa suke
    shakkar tunkararsu da soyayya.

    Wata mata mai aikin soji ta bayyana cewa sama da
    shekara 4 kenan tana aikin soji amma ko da sau
    daya babu namijin da ya taba tunkarar ta da
    maganar soyayya balle har ta kai su ga maganar
    aure.

    Matar ta bayyana wa 'yan jarida cewa "kasancewa ta
    soja ba yana nufin ba ni da bukata irinta kowacce
    ba ne, kuma tayaya ne ma zan samu na yi aikina
    cikin nutsuwa yayin da na rasa muhimmin bangaren
    rayuwa ta na mace."

    No comments