Hadiza Gabon Ta Maidawa Da Wani Matashi Martani
Ko Za Ka Baiwa Tsoho Shawara Ya Yi Wa Tsohuwa
Ritaya Ya Auro Ni?, Martanin Hadiza Gabon Ga
Wani Matashi Da Ya Nemi Ta Yi Aure
Jarumar Finafinafin Hausa Hadiza Aliyu Gabon, Ta
Mayarwa Wani Matashi Martani A Shafinta Na
Twitter.
Shidai Matashin Mai Suna M. Bash Ya ba ta
Shawarar Cewa, Ta fidda Miji Ta yi Aure Tunda Ta
Girma, A Daidai Lokacin Da Ta Sanya Wani Hotonta
A Shafin nata Na Twitter.
Furucin Matashin Bai yi wa Hadiza Gabon Dadi ba,
Inda Ta Mayar mishi Da Raddin Cewa, Ya je Ya
kaiwa Mahaifinsa Shawarar Ya yi wa Mahaifiyar shi
Ritaya, In Ya so Sai Ya Maye Gurbin Mahaifiyarta
shi Da Ita.
Mun yi Kokarin Jin Ta bakin Hadiza Gabon Don Jin
Komai Ya Harzuka ta Har tayi Wannan Raddin, Duk
Da Al'umma Suna Mata Kallo Mai Hakuri Kuma
Wacce Ta Shahara Wajen Tallafawa Al'umma Masu
Karamin Karfi, Sai Dai Hakar mu Bata Cimma Ruwa
ba, Domin Mun yi Ta Kiran Lambarta Amma A Rufe,
Kuma Mun Aike mata Da Sakon Shi ma Har yanzu
Bai shiga ba.
Duk Wanda Yak eso Ya ga Wannan Raddin Na
Hadiza Aliyu Gabon Sai Ya Ziyarci Shafinta Na
Twitter.



No comments