Kiwon Lafiya Yadda Cutan Hana Mata Sukuni Ta Hana Wata Mace Sukuni A Rayuwa
Endometriosis cuta ce da ke azabtar da masu
fama da ita, ba sai lokacin ganin al'ada ba.
Ko wace mace daya cikin goma na da cutar
endometriosis, amma a Burtaniya sai da aka dauki
shekara bakwai kafin likitoci su gane cutar.
Endometriosis wata tsoka ce mai kama da ta cikin
mahaifa take tsiro wa a wasu sassa na jiki, inda
take janyo mummunan tasiri.
Amelia Davies na da shekara 12 a lokacin da ta
fara al'ada.
Ba a jima ba ta fara taraddadin
zagayowar ranar al'adarta.
"A wasu lokutan lamarin kan kai ga ba na iya zuwa
makaranta.
Nakan kasa fita tsawon kwanaki masu
yawa.
Azabar ba ta misaltuwa, kuma akwai iri
daban-daban - mai suka, mai daure ciki da mai
kuna.
Lamarin ya kai munzalin da ba na iya tafiya
ko ma sauka daga gado."
Hukumar Lafiya ta Burtaniya, NHS ta fitar da wasu
sabbin matakai da za su rage jinkirin da mata masu
fama da cutar ke fuskanta kafin a gane tsananin
cutar.
'Babu maganin cutar Endometriosis da ta
gallabi mata'
Nigeria: Yadda tsarki da sabulu ya jawo wa
wata mace matsala
Cuta mai raunatarwa
Amelia ta fara sanar da likita alamun da ke
damunta, daga baya ta ga wasu likitocin wadanda
suka ce ba su gane abin da ke damunta ba.
"Daga baya sai suka tura ni wani asibiti domin a
dauki hoton jikina."
"Binciken ya nuna cewa tana da wani ciwo a
mazaunin kwai da ke cikin mahaifarta, da kuma
cutar endometriosis.
Idan mata mai fama da endometriosis na al'ada,
wannan tsokar da ta fito a wasu sassa na jikinta
ma na fitar da jini, wanda ke sa mata
matsananciyar azaba da wasu matsalolin da ba
kasafai a kan same su ba.
Wasu matan kan yi fitsarin jini a daidai lokacin da
suke al'ada. Wasu ma kan yi tarin jini idan tsokar ta
fito a huhunsu.
Likitan Amelai ya bata shawarar ta rika shan
maganin hana haihuwa domin samun waraka daga
cutar.
A halin yanzu tana shan maganin, kuma shekararta
biyu kenan ba ta ga al'adarta ba.
Amma Amelia wacce yanzu ke da shekara 18 da
haihuwa kuma tana zaune a yankin kudancin birnin
Landan ta ce duk da haka, tsokar endometriosis na
janyo mata radadi kullum.
Ta fara rubuta halin da take ciki a shafinta na
intanet .
"Har yanzu na kan fuskanci matsaloli idan ciwon ya
tashi, kuma yana azabartar da ni."
Wata kwararriyar likitar cututtukan mata, Caroline
Overton, wacce ta taimaka wajen rubuta sabbin
matakan da hukumar lafiya ta Burtaniya, National
Institute for Health and Care Excellence, ta ce:
"Babu maganin cutar endometriosis, sabili da haka
tallafa wa masu fama da ita su iya rayuwa da cutar
na da muhimmanci."
Ita kuma Emma Cox ta kungiyar Endometriosis UK
cewa ta yi: "Tasirin da rashin gane cutar a rayuwar
mata masu fama da ita na da yawa - daga iliminta
zuwa aikinta da rayuwarta a gida.
"A yawancin lokuta, matan kan jure zolayar wadanda
ba su san halin da suke ciki ba, inda su kan ce
musu babu wata matsala da ke damunsu".
Bayani kan Endometriosis
Ba a iya samun endometriosis daga mai fama da
shi, kuma babu wani abin da ki ka yi da ya kawo
miki cutar.
Matan da suke daidai shekarun haihuwa daga ko
wane irin jinsi na iya kamuwa da cutar.
Cuta ce mai daukar lokaci kafin a iya gane ta, kuma
ta kan dade a jikin masu cutar.
Alamun cutar sun hada da ciwon kugu, al'ada mai
azabarwa da gajiya, da kuma jin zafi a lokacin
jima'i.
Ba lalle ba ne likitanki ya iya gane kina da cutar,
kuma ba dole ne gwaje-gwaje su bayyana cutar ba.
Akwai magungunan da suka hada da na hana
daukar ciki da kan taimaka wa masu fama da
azabar cutar.
A kan yi wa wasu matan tiyata domin cire tsokar
daga sassan jikinsu, wasu kuma ana cire
mahaifarsu ce baki daya.
Mata masu fama da endometriosis na iya haihuwa -
an kiyasta kashi 70 cikin dari na mata masu cutar
da ba ta yi tsanani ba na iya samun juna biyu ba
tare da amfani da magani ba.
Source By Bbcha7sa

No comments