Jarumar Kannywood Hauwa Waraka Tace Zata Hadama Duk Wanda Zai Aureta Lefe
Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa
Abubakar wacce aka fi sani da Hauwa
Waraka, ta ce tana yawan fitowa a
mutuniyar banza ne saboda ta nunawa
al’umma illar rashin kirki.
“Ina fitowa a matsayin karuwa ko ‘yar
kwaya ko ballagaza ne saboda na
ilimantar da mutane domin su guji zama
irin wadannan mutane”, in ji Hauwa
Waraka, a hira ta musamman da BBC
Hausa.
Ta kara da cewa, “Ban taba karuwanci ba
kuma ban taba yin hulda da karuwai ba,
amma idan ina taka rawa a matsayin
karuwa kai ka ce ni tsohuwar magajiya
ce.”
A cewar jarumar bai kamata mace da za
ta fito a matsayin karuwa “a gan ta sanye
da hijabi ba.
Ko kuma macen da ta fito a
matsayin ‘yar shaye-shaye a gan ta ras
kamar mutuniyar kirki ba.
“Shi ya sa za ka gan ni ina keta rashin
mutunci a fim kamar da gaske. Kuma
abin da ya kamata kenan.”
Hauwa Waraka ta ce sau da dama tana
zuwa unguwa mutane suna “cewa wacce
irin kwaya ko wiwi ko taba za su kawo
min na sha.
Ba su san cewa ban taba
shan kayan maye ba; wallahi ko taba ban
taba sha ba.
Duk abin da ka ga ni a fim
ne”.
Da aka tambaye ta kan zargin da ake yi
wa ‘yan fim na luwadi da madigo,
jarumar ta ce akwai bara-gurbi sosai a
cikinsu “kamar yadda akwai su a cikin ko
da Malaman addini amma bai kamata a
yi mana kudin-goro ba.”
Ta bukaci mutane su rika yi musu uzuri
musamman ganin cewa su ma mutane ne
kamar kowa.
Hauwa Waraka, wacce ta ce tana son yin
aure, ta kara da cewa “kai ma wakilin
BBC idan kana sona ka fito. Wallahi
aurena ba zai yi tsada ba. Kai, ni zan
hada maka lefe ma akwati shida idan
kana so.
“Ko da yake na san tsoron matarka kake
yi kada ka je gida ta ki bude maka
kofa”…(dariya).
Source By BBCHAUSA


No comments