Shugaban Kasa Muhammad Buhari Yayima Jama,ar Nigeria Barka Da Sallah - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Shugaban Kasa Muhammad Buhari Yayima Jama,ar Nigeria Barka Da Sallah

    SAKON GORON SALLAR SHUGABA BUHARI GA 'YAN
    NAJERIYA.



    Ya 'Yan Uwana 'Yan Najeria
    Ina mai matukar taya ku murna dukkanin ku,
    musamman ma Musulmai daga cikinku na wannan
    ranar Sallar Idi babba (Eid-El-Kabir) na wannan
    shekarar.


    Haka kuma ina taya 'Yan uwa musulmanmu maza
    da mata da suke kasa mai tsarki (Makka) a yanzu
    haka domin gudanar da aikin Hajjin wannan
    shekarar.


    Amma daga farko ina so zan yi amfani da wannan
    damar domin in yi muku godiya bisa irin addu'oin
    da ku ka yi ta gudanarwa a kaina domin samun
    lafiyata da kuma fatar alheri da kuma murna
    dawowa ta Nijeriya.


    Hakika addu'oinku da kuka dukufa kukaita
    gudanarwa akaina wacce da hanada musulmanku
    da kiristoci daga cikinku dama masu mabanbantan
    ra'ayin siyasa dama kabilu daban-daban daga
    cikinku, hakika sun kara mun kwarin guiwa da kara
    dagewata sosai dama gwaunatinmu domin gina
    wannan kasa tamu ta cigaba.


    Daga bangaren shagalin bikin sallar layyar wannan
    shekarar, ina rokon dukkanin 'Yan Najeriya da mu
    aje banbance-banbancen dake tsakaninmu, mu
    watsar da tsana da tsangwama mu rungumi
    zumunci da abota da 'Yan uwantaka da kuma hadin
    kai domin mu ciyarda kasarmu Najeriya gaba
    Daga bangaren musulmi na duniya kuma, manufar
    wannan bikin shine tuna irin jarabawar da ubangiji
    yayiwa annabi Ibrahim na yanka dansa ne da kuma
    irin mika wuyar da yayi wurin biyayya ga umarnin
    mahaliccinsa ne.


    Kamar yadda muke cike da farin cikin wannan bikin,
    inada yakinin wannan kasa tamu zata samu cigaba
    cikin sauri ta kowani bangare idan mukayi koyi da
    halayen annabi Ibrahim ta hanyar sadaukar da kai,
    hakuri, son juna, kwazo da kuma biyayya ga
    umarnin ubangijinmu da kuma kiyaye dokokin
    hukuma
    Dole ne mu koyawa kanmu son juna da kuma
    daukar kanmu a matsayin 'Yan uwa maza da mata
    wadanda mukeda tarihi iri daya kuma dole ne mu
    zama kamar yadda wata karin magana ta 'Yan Afrika
    take cewa "Iyalai kamar bishiya ce, za ta iya
    lankwashewa amma ba za ta karye ba"
    Haka kuma har wayau dai, ina mai tabbatar muku
    cewar wannan gwaunatin wacce ta dauki harkar
    tsaron kasa, tattalin arziki da walwalar yan kasa a
    matsayin ababe masu muhimmanci data sanya a
    gaba, ba zata taba gajiyawa ba har saita cimma
    gurinta na samarda sabuwar Najeriya mai cike da
    zaman lafiya tattalin arziki mai yalwa da kuma
    cigaban jama'a.


    Ina yi wa kowa da kowa barka da sallah kuma a yi
    biki lafiya.


    MUHAMMADU BUHARI
    31/AGUSTA/2017.


    No comments