Babban Bankin Raya Kasa Na Afrika Zai Zuba Jari Dan Bunkasa Aikin Noma A Africa - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Babban Bankin Raya Kasa Na Afrika Zai Zuba Jari Dan Bunkasa Aikin Noma A Africa

    Bankin Raya Afrika Zai Zuba Jarin Bunkasa Aikin
    Noma A Afrika.

    Bankin raya kasashen Afirkaya ce zai zuba jarin Dala
    biliyan 24 nan da shekaru 10 domin ganin nahiyar
    Afirka ta bunkasa aikin noma da samar da abinci
    maimakon dogaro da kasashen duniya.

    Shugaban Bankin Akiwunmi Adeshina wanda ya
    bayyana haka ya ce za a kaddamar da shirin ne a
    karkashin shirin bankin mai taken Ciyar da Afirka.

    Adeshina ya kuma ce bankin yana kokarin ganin ya
    samarwa manoma kasuwannin da suka dace da za
    su dinga taimaka wa manoman wajen samun ribar
    amfanin gona sabanin yadda ‘yan kasuwa ke yi.

    A ranar 4 ga Satumba Bankin raya Afrika zai
    jagoranci wani babban taron nazarin raya Afrika a
    Abidjan a bangaren wadatuwar abinci da samar da
    ayyukan yi a fannin noma.
    Bankin yana fatar kashe dala tiriliyan 1 zuwa 2030 a
    karkashin shirin.



    No comments