Gwamnatin Tarayya Ta Aminci A Fara Aikin Wutan Lantarkin Hawan Mambila - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Gwamnatin Tarayya Ta Aminci A Fara Aikin Wutan Lantarkin Hawan Mambila

    Gwamnatin Tarayya Ta Amince A Fara Aikin Samar
    Da Wutar Lantarki Ba Manbila
    ...kimanin naira bilyan 5.5 za a kashe a aikin

    Gwamnatin Nijeriya ta amince da bada kwangilar
    gina tashar samar da wutar lantarkin Mambila akan
    kudi sama da dala biliyan 5.5 domin samar da
    megawatt 3,050 a Gembu dake jihar Taraba.


    Ministan ayyuka da makamashi Babatunde Fashola
    ya ce Majalisar ministocin a karkashin shugaba
    Muhammadu Buhari ta amince da aikin wanda aka
    fara batun sa shekaru 45 da suka gabata ba tare da
    aiwatarwa ba.


    Fashola yace za’a kwashe watanni 72 ana gudanar
    da aikin wanda zai shafi gina madatsun ruwa guda
    4 da gina turakun samar da wutar da zasu ci
    kilomita 700.


    Ministan ya ce gwamnatin Nijeriya da bankin China
    za su bada kudin da za’a gudanar da aikin.





    No comments