Matar Shugaban Kasar Nageria Aisha Buhari Ta Halarci Taron Bude Wani Katafaren Asibiti Qatar - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Matar Shugaban Kasar Nageria Aisha Buhari Ta Halarci Taron Bude Wani Katafaren Asibiti Qatar


    Aisha Muhammad Buhari matar mai girma shugaban kasan Nigeria Muhammad Buhari ta halarci wani bikin bude wani katafaren Asibitin bincike na mata na dakanan yara a Doha Qatar ranar 13 ga wannan wata da muke ciki.


    Aisha Buhari dai itace ta kasance babban bakuwa a wannan biki kuma ta samu cikakkiyar tarba ta musamman tare da karramawa a matsayinta na babbar bakuwa.


    Ba haushe na cewa ko wani gauta jane, dan hakane itama matar shugaba kasa tabi sahun mijin nata wajen ganin sun kyau tatawa kowa bama Nigeria kadai ba harma da duniya baki daya.


    Domin kuwa amsa gayyata wajibi ne ga dukkan musulmai kamar yadda addini ya tanazar dan hakane yasa matar shugaban kasar itama bata kasa amsa goron gayyata ba.


    Muna Aishat Buhari fatan Alkhairi tare da fatan dawowa gida lafiya.



    No comments