Halimat Atete Tana Murnan Zagayowar Ranar Haihuwanta - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Halimat Atete Tana Murnan Zagayowar Ranar Haihuwanta


    A yau ne fitacciyan jarumar fina-finan Hausa wacce akafi sani da Halimat Atete (Dakin Amarya) take murnan zagayowar ranar haihuwata (Birthday).

    Ita dai jaruma Halimat Atete haifafiyar garin Borno ne sannan ta fara haskawa a fina-finan Hausa a sheka dubu biyu 2000.

    Wanda yanzu haka tana da shekara goma sha takwas da fara haskawa a fina-finan hausa.


    Sannan an haifi jarumar ranar 26th/November/1988 wanda yanzu haka tana da shekara 30 kenan da haihuwa.

    Jaruma Halimat Atete tayi fina-finai da daman kamar su; Dakin Amarya, Wata Hudu, Maza Da Mata, Hannu Da Hannu, Kawayen Amarya, da dai sauran su.

    Sannan jaruma Halimat bata tsaya kawai a fitowa a film ba kadan domin kuwa jarumar ta kasance mai daukan nauyin fina-finan ta dau nauyin fina-finai da daman tun a baya harya zuwa yanzu.


    Kadan kenan daga cikin tarihin jaruma Halimat Atete, da haka shafin mu yake taya jaruma Halimat Atete murnan zagayowar ranar haihuwa.

    Ku Kasance Tare Da Shafin Mu Domin Samun Labarai Da Dumi-duminsu.

    No comments