Ana Zargin Makaman Da Sojojin Nigeria Ke Amfani Dasu Tsofaffin Yayi Ne
Gaskiya yana dakyau Baba ya dau mataki sosai. Da alamu har yanzu makaman da sojojin Nigeria ke amfani dasu duk tsofaffin yayi ne kuma kananu wadanda sunyi kankantar ace dasu ake tunkarar manyan yan ta'adda kamar yan boko haram.
Sanin kowa ne ana fitar da kudi sosai wajen siyan makamai don yaki da ta'addanci, amma a duk lokacin da aka gwabza wani kazamin yaki sai kaga kamar ma babu wasu sabbin makamai da aka baiwa sojojin.
Faifan bidiyon yadda yan ta'addan boko haram suka kashe sojojin da ake kiyasin cewa adadinsu ya haura 70 da kuma yan wasu hare-hare na baya-bayan nan ka iya tabbatar da batutuwa na..
Allah yayi mana maganin duk abinda yafi karfinmu ko yake neman yafi karfin mu...
wanda yarubuta Deen yashe dabai
No comments