Yusra Zainab Raga Na Murnar Cika Shekara Shida Da Haihuwa
Babban 'yar jaruma Zainab Umar kenan wacce akafi sani da (Zainab Raga) mai suna Yusra tana murnar cika sheka shida (6) da haihuwa.
Zainab Raga dai na daya daga cikin jarumawa mata wayanda suka haska a duniyar film din hausa a shekarun baya.
Jaruma dai ta bawa masana'antar fina-finan Hausa gudunmawa wanda duk wani mai kallon film din hausa yaga irin gudun mawar data bayar wajen ganin masana’antar taci gaba.
Jarumar tayi aure ne lokacin da take haskawa bawai lokacin da tauraronta ya dushe ba kamar yadda wasu sukeyi sai sunga duniyar ta dainayi dasu.
Zainab Raga dai ta bawa marada kunya kamar yadda mutane suke yawan cewa su yan film din hausa basa iya zaman aure sai gashi ita tayi aure kuma ta zauna lafiya lau a gidan mijinta.
Gashi yau an wayi gari har tana da kyakkyawar budurwa wacce yau take cika shekara shida (6) dahaihuwa.
Jaruma Zainab Umar Raga ta taya 'yar nata murnar zagayowan ranar haihuwa tare dayi mata addu'ar samun rayuwa mai albarka ga kadan daga cikin addu,o'in data yiwa 'yar nata.
Alhamdulillah.... Allah yakare ki da kariyarsa... Allah yatsare ki da tsarewarsa.... Allah ya inganta rayuwarki.... Allah yabaki ilimi mai amfani.... Allah yayimaki albarka.... Happy birthday my love❤❤❤❤❤
Da haka shafin mu yake mika sakon taya murnar zagayowar ranar haihu ga Yusra Allah ya karo shekaru masu amfani HAPPY BIRTHDAY TO YOU YUSRA.








No comments