Wata Jami,a Mai Suna ISM Adonai University Ta Karma Malaman Izala
An Karrama Wasu Malaman Izala A Jamhuriyar Benin.
Wata jami'a mai suna "ISM Adonai University" a birnin Cotonou ta kasar Benin Republic, ta karrama manyan Malaman Izala da digirin digirgir. Cikin wadanda Jami'ar ta karrama daga sassa daban daban a fadin duniya harda shugaban IZALAR Naijeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau, da Babban Sakataren IZALA Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Da Sarkin Damaturu da kuma Sarkin Machina.
Jami'ar ta karrama wadannan Malaman ne bisa jajircewa da suka yi wajen wa'azi a kasashen Afrika da yankin Turai, tare da jinkan marayu da taimakon nakasassu wajen tallafa musu da kafafu da hannuwan roba. An yi wannan gagarumin Lamari ne a jiya Asabar a cikin filin jami'ar da ke kasar Togo.
Madogara: Dr. Mansur Ibrahim Sokoto



No comments