Kannywood Meyasa Auren Yan Film Din Hausa Yake Saurin Mutuwa - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Kannywood Meyasa Auren Yan Film Din Hausa Yake Saurin Mutuwa


    Tsohuwar Jarumar Fina-finan Hausa kenan tare da mijinta da yaranta wacce idan mai karatu bai manta ba ake kiranta Safiya Musa.

    Jaruma ta kasance daya daga cikin fitattun jarumawa mata da akeji dasu a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood a baya.

    Kamar yadda mutane keta yada jita-jitan cewa yan film din hausa basa iya zaman aure sakamako yadda wasu daga cikinsu da sunyi aure ba,a dadewa sai kaga an samu matsala wanda kuma idan ka duba zakaga wasu laifin sune wasu kuma laifin daga mazajen da suka aura ne.

    To ai daman duk wanda yahau motar kwadayi to fa zata saukeshi a tashar wulakanci kamar yadda bahaushe ya fada, mafi yawa dama auren da kaga anyishi bai dade ba ya mutu to idan ka duba zaka badan Allah akayishi ba anyishi ne saboda abun duniya shi kuwa daman abun duniya mai karewa ne kamar yadda da zaran ya gama biyan bukatarehi sai kuma wulakanci ya biyo baya daga nan sai kuma saki ya biyo baya.

    Idan mai karatu yana biye damu kwanakin baya mun jiyo wata daga cikin shahararrun jaruwa mata wacce duniyar Masana'antar Fina-finan Hausa ta dama da ita a baya wato jaruma Fati Muhammad tana fadin cewa; Auren Sha'awa ake musu baiwai ana aurensu saboda da Allah da Annabi bane.

    Kwanamin baya idan ba,a manta ba munjiyo wata kuma daga cikin jaruwan ita kuma danasanin shiga ta biyu takeyi sakamakon rashi jituwa tsakaninta da abokiyar zamanta.

    Idan muka duba mukagani zamuga cewa lallai duk abunda aka ginashi da zuciya daya insha Allahu zaiyi karko dan kaucewa tarkon dana sani sai mu guji abun duniya mu tsaya mu karanci mai son mu tsakani da Allah bawai dan kyan mu ba kodan wani abunda muke dashi ba.

    Yanzu idan muka duba wannan Jaruma wato Safiya Musa idan mai karatu bai mata ba a baya jama,a sunyita fadin cewa bazata iya zaman aure ba amma da yake ta tsaya tabi a hankali batabi son zuciya da son abunda duniya ba gata nan tana zamanta cikin kwanciyan hankali tare da iyalanta wannan itace soyayya ta gaskiya ba son zuciya ba.

    Da haka mukewa jamar fatan alkhairi Allah kuma ya kara basu zaman lafiya ita da mijinta Allah kuma ya shirya mata zuri'a ya kuma albarkace su.

    No comments