Allah Yayiwa Uwar Marayun Zaria Dakewaye Rasuwa
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un
Uwar Marayun Garin Zaria Kuma Hadimar Musulunci, Ta Rasu
Allah ya yi wa kakar marayu kuma Shugabar kungiyar Nisa'ussunnah ta Zaria, HAJIYA MAHADIYYA BABA AHMAD rasuwa yau da safen nan.
Hajiya Mahadiyya wacce diya ce ga Marigayi Sheikh Baba Ahmad kuma Yaya ga Shugaban Ma'aikatan Shugaban Majalisar dattawa Dr. Hakeem Baba Ahmad ta hidimtawa addinin Musulunci matuka ta hanyar kafa cibiyoyin da taimaka ma kungiyoyin addinin musulunci.
Fatan mu Allah ya amshi kyawawan ayyukanta ya gafarta kurakuranta, ya sa Aljanna ta zama makoma gareta.
No comments