Kannywood Ni Ba Mawakin Siyasa Bane Kuna Bana Wakar Nana Aminu Ladan (Alan Waka)
Wata Jaridar Yanar gizo ta mai suna Rariya ta wallafa a shafinta cewar Sanannen mawakin zamani na harshen hausa Alhaji Aminu Ladan Abubakar wanda akafi sani da suna Alan Waka, ya bayyana dalilanshi wadanda suka sanya jama'a basu ga fuskar sa ba a cikin jerin gwanon mawaka wadanda suka rera wakoki a babban taron APC wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja kwanakin baya, inda ya tabbatar da cewar shi mawaki ne na kishin kasa ba na siyasa ba.
Alan Waka yayi wannan bayani ne lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Kaduna wajen kaddamar da faifan waka na wani mawaki mai suna Yahaya Makaho, Wanda ya gudana a dandalin Murtala Muhammad, akan rashin jin duriyarshi a yayin wannan taro wanda ya tara mawaka.
Mawakin ya cigaba da cewar babban abinda yake bukatar mutane su fahimta game da shi shine, shi ba mawakin siyasa ko dan nanaye ba ne, shi mawaki ne wanda yake gudanar da wakarshi akan kishi da cigaban jama'a, kuma kamar yadda jama'a suka sani shine ya bayar da tashi gudummuwa a yayin zaben 2015 akan Allah ya kawo sauyi wanda ake zaton zai taimaki Arewa da Nijeriya, kuma a wancan lokaci babu wanda ya sanya shi, shi ya sa kanshi, amma mawakan da ake gani a tarukan siyasa mawaka ne masu Neman kudi wajen 'yan siyasa bambancin dake tsakani na da su kenan inji shi.
No comments