Kalli Hotunan Kadan Daga Cikin Matan Da Suke Neman Auren Dangote - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Kalli Hotunan Kadan Daga Cikin Matan Da Suke Neman Auren Dangote



    Bayan wata shela:Wasu matan Najeriya sun gigice da son auren Dangote

    A wannan zamani da muke ciki mafi akasarin 'yan mata basu da wani buri da wuce mallakar namiji mai tarin dukiya ta yadda za su fantama son ransu.
    .Hakan ce ta kasance a lokacin da labarin neman matan aure da mai kudin Afrika Alh.Aliko Dangote ya shelantawa duniya, inda mata da dama a Najeriya suk bayyana ra’ayoyinsu akan lamarin.

    A makon nan ne dai Jaridar Financial Times (FT) ta wallafa cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote na neman matar da zai aura.

    Wannan ya sa wadansu mata musamman a kafafen sada zumunta suka rika bayyana bukatarsu ta neman auren attajirin, wanda a yanzu ba shi da mata.

    Aisha Falke mai shafin Instagram na northern_hibiscuss ta wallafa labarin Dangoten kuma ta shaida mana cewa ta samu dimbin sakonni daga mata wadanda suke neman attajirin ya aure su.

    Aisha ta kara da cewa:
    "Tun a ranar da na sanya wannan labarin a shafina, mata suke ta turo min sakonni har da kiran waya, cewa na yi musu hanya."

    "Sun yi tsammanin ko ta wajena ya zo neman auren, ba su san cewa ba ni da kowacce irin alaka ko kusanci da Dangote ba,
    labari kawai na gani na sanya musu."

    Ga ra'ayoyin wadansu mutane da muka samu da shafin Instagram a Najeriya:

    1, Zakiya musa jibril

    "Tirkashi ai har sai ya rasa wadda zai zaba don zai samu issasun masoya."

    2, khaxeenerh_yaree

    "Tou ta ina ake samo shi bai ba da inda za'a same shi ba."

    3, jrabdul malik

    "zan iya nema wa kanwata(aurensa)?
     don ba ta kan Intanet a yanzu...tana da gogewa kan zaman aure na tsawon shekara hudu, na bukace ta da ta kashe aurenta tun bayan da na ji labarin nan."

    Sai dai kuma akwai wadanda suka yi wa attajirin addu'a da kuma ba shi shawara, kamar haka:

    hafcert hassan:

    "Allah ya ba shi ta gari wacce za ta so shi tsakani da Allah."

    No comments