Gobara Daga Teku Wata Sabuwar Masifa Ta Billo A Jalingo Taraba State - Duniyarfim.com
  • Breaking News

    Gobara Daga Teku Wata Sabuwar Masifa Ta Billo A Jalingo Taraba State



    GOBARA DAGA KOGI A GARIN JALINGO

    Wani masifan da yab'allo cikin matasanmu ayau shine, yadda zakaga kusan kowane unguwa a faďin jalingo tanada wassu guggan matasa wadda basuda aiki illah bayan sati daya zuwa biyu suyi gangami wajen tare Wata babbar hanya sufarma mutane da sara da suka batare da kamusu laifin komaiba, da sunan SHARA kamar yadda ake gani a fina finan INDIYA, sukan fitowane sama da mutum 15 zuwa 20 da niyar duk wadda suka haďu dashi a wannan rana kodai yakwana a asibiti kokuma barza'u, ba babba ba yaro ba mace ba namiji, kan mai uwa da wabi, a duk lokacin da suka fito wannan operation ďin nasu zakaga manya da yara suna gudun famfalak'i dan tsira da rayukansu,


    Kusan zan iya cewa sun maida wannan abu tamkar sana'a domin duk lokacin da suka fito wannan abu mai suna SHARA ďinbin jama'a ne suke rasa wayoyin hannunsu wassu kuma kuďaden dake Aljihunsu,

    A wani b'angaren kuma matasan sukan yin amfani da keke nafek bayan sun daukeka kuna cikin tafiya fasinjan gefenka wadda kake zaton tafiyansu ba daya bane da mai keken zai ciro wuk'a inma kabayar a hankali su saukek'a kayi tafiyarka kokuma yasokeka da wuk'a su ďebe abun da yake jikinka sujefar dakai suyi tafiyarsu


    Abunda zai baka mamaki shine, dukka wannan abu yana faruwane a cikin garin jalingo babbar birnin jahar Taraba, inda gomna yake, amma kullum abun k'ara tsamari yake, kojiya da dare Matasan Unguwar Gadan Bobboji sun fito Operation ďinsu mai suna SHARA inda sukaci karensu ba babbaka suka hau sharee Jama'a, sai dai naji antura police sun tarwatsasu daga baya,

    Ina kira ga daukacin masu faďa aji musamman Sarkin Jalingo da manyan Malamai da hukumomi dasu tashi tsaye wajen ganin bayan wannan matsala tunkafin wankin fula yakaimu dare.

    No comments